Yayin ganawarsu, Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su kafa dangantakar aikin soja a tsakaninsu bisa ka'idojin hana aukuwar rikici, mutunta juna, hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, ta yadda za a iya inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa dukkan fannoni yadda ya kamata. Ya ce hakan zai iya warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu ta hanyoyin da za su dace, kuma ya ciyar da dangantakar kasashen gaba ta hanyar da ta dace.
A nasa bangaren, Mr. Hagel ya nuna fatan cewa, za a iya ciyar da kafuwar dangantakar aikin soja ta musamman a tsakanin kasashen biyu gaba, don haka kasar Amurka na son karfafa shawarwari a tsakaninta da kasar Sin don kara fahimtar juna, ta yadda za a iya inganta dangantakar kasashen biyu, musamman ma a bangaren aikin soja tsakanin kasashen biyu. (Maryam)