in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na kokarin kiyaye dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin
2014-01-03 16:15:49 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Madam Marie Harf ta fadi a ran Alhamis 2 ga wata, ranar da ya cika shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin Amurka da kasar Sin cewa, Amurka za ta ci gaba da inganta dangantaka mai dorewa tsakaninta da Sin cikin dogon lokaci.

Madam Marie Harf ta ce, Amurka na fatan ganin kasar Sin ta samu bunkasuwa da wadata, tare kuma da taka rawarta yadda ya kamata a yankin Asiya-Pacific.

A gun taron manema labaru da ma'aikatar ta yi a wannan rana, Madam Harf ta bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ba iri na yin takara da juna ba ne kawai, illa kasashen biyu za su ci gaba da habaka hadin kai bisa moriyar dake jawo hankalinsu, ban da haka, Amurka za ta karfafa dangantaka mai dorewa tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci a fannin diplomasiyya, tattalin arziki, aikin soja da dai sauransu.

Bugu da kari, Madam Harf ta nuna cewa, ko da yake, akwai wasu bambancin ra'ayi tsakanin Sin da Amurka, duk da haka bangarorin biyu sun yi hadin kai kan wasu manyan batutuwa, kamar yadda mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya furta a kwanan baya, cewa ba za'a bari bambancin ra'ayi ya lalata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba, don haka ya kamata kasashen biyu su bayyana ra'ayinsu a fili tare da yin hadin kai mai yakini kan wasu manyan batutuwa.

An kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka a hukumance a ran 1 ga watan Janairun shekarar 1979. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China