A yayin taron, Mr. Cui ya bayyana cewa, akwai bambance-bambance da dama dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka dangane da al'adu, tsarin zamantakewar al'umma, da kuma yanayin bunkasar tattalin arziki da sauran fannoni, wannan ya sa, ake samun bambancin ra'ayoyi tsakanin kasashen biyu wajen warware harkokin kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya, duk da haka, kasashen biyu na kokari wajen neman hanyoyin cimma ra'ayi daya kan wasu ayyuka, ta yadda za a samu moriyar juna da kuma karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Ya kuma nuna fatan cewa, kasar Sin da kasar Amurka za su iya mai da hankali kan samun moriyar juna, daukar nauyijn da ke wuyansu na yin hadin gwiwa cikin harkokin kasa da kasa, bisa ka'idojin girmama juna da kuma hadin gwiwa.
Ban da wannan kuma, a yayin wannan taron, Mr. Cui ya kuma yi allah wadai da ziyarar da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya kai wurin ibadan Yasukuni da ake takaddama a kai, inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su tsaya tsayin daka wajen nuna adalci kan lamarin ba tare da manta da tarihi ba
Mr. Cui ya kuma jaddada cewa, bai kamata gamayyar kasa da kasa su amince da manufar Shinzo Abe ba, wadda za ta jagoranci jama'ar kasar Japan kan wata hanyar da ba ta dace ba. Kuma ya kamata a kiyaye tsarin gamayyar kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu tare da kiyaye yanayin zaman lafiyar kasashen da yakin ya shafa, kamar su kasashen Sin, Amurka, Koriya ta Kudu da dai sauransu. (Maryam)