Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya iso nan birnin Beijing da safiyar Juma'ar nan 14 ga wata, don fara ziyarar aiki ta kwanaki 2 a kasar.
Bisa labarin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayar, an ce, wannan ziyara ta biyo bayan gayyatar da takwaransa na kasar Sin Wang Yi ya yi masa.
A yayin wannan ziyara, jagororin biyu za su yi musayar ra'ayi game da alakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, da sauran batutuwan da suka dora muhimmanci a kan su.
Yayin wannan ziyararsa daga ranar 13 zuwa 18 ga wata John Kerry, zai ziyarci kasashen Koriya ta Kudu, da Sin, da Indonesiya da kuma kasar Saudiyya. Kafin zuwansa nan kasar Sin, sai da ya kammala ziyara a kasar Koriya ta Kudu.(Bako)