Dangane da lamarin, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau ranar Jumma'a 7 ga wata a taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, jami'an Amurka sun soki kasar Sin ne sakamakon wasu jita-jitan da masu tsattsauran ra'ayi na kasar Japan suka baza, na cewa, wai kasar Sin ta yi shirin shata sassan tsaron sararin sama a tekun Kudu. Don haka yadda jami'an ba su tabbatar da jita-jitan ba ya nuna cewa, ba su sauke nauyin da ya kamata su sauke ba.
Hong Lei ya kuma sake jaddada cewa, a matsayinta na wata kasa mai ikon mulkin kasa, kasar Sin na da ikon daukar dukkan matakan da suka wajaba domin tabbatar da tsaronta a sararin sama, ciki had da shata sassan tsaron sararin sama, abin da ya sa bai kamata a yi soki lamarin ba.(Tasallah)