Kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta daina sayar wa mahukuntan Taiwan makamai nan da nan ba tare da bata lokaci ba, ta kuma dauki hakikanin matakan kiyaye kyakkyawan ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2 da kuma kyakkyawar bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yansheng ya sanar da hakan a yau ranar Alhamis 27 ga wata a wajen taron manema labaru da aka saba shiryawa duk rana a nan Beijing, dangane da tambayar ra'ayin kasar Sin a kan isowar jiragen sama masu saukar ungulu da dama a Taiwan, wadanda rundunar Taiwan ta saya daga hannun Amurka a kwanan baya.
Mista Geng ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kin yarda da gamayyar kasa da kasa da su sayar wa Taiwan makamai. Don haka kasar Sin ta kalubalanci Amurka da ta bi manufar "kasar Sin daya tak a duniya" da kuma wasu muhimman manufofi guda 3 da Sin da Amurka suka daddale dangane da yankin Taiwan, sannan ta daina sayar wa Taiwan makamai, a kokarin kiyaye ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da Amurka da kuma bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.(Tasallah)