in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka
2014-02-14 16:27:29 cri

A ranar Juma'ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry a nan birnin Beijing.

Kerry ya yi amfani da ganawar tasu, wajen mika gaisuwar taya murnar shiga sabuwar shekara, da shugaba Obama ya aiko ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, ya ce shugaba Obama yana fatan nan ba da dadewa ba, zai sake yin shawarwari da takwaransa na kasar Sin, tare da fatan kara tuntubawar sa cikin wannan sabuwar shekara.

A nasa tsokaci shugaban Xi ya mai da sakon gaisuwar sa ga takwaransa na Amurka, yana mai cewa kasar Sin za ta dukufa ka'in da na'in, wajen karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Mr. Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su kiyaye mu'amalar da ke tsakanin manyan jami'ai, da tuntubawar juna bisa manyan tsare-tsare, don tabbatar da nasarar shawarwari da ke tsakanin kasashen Biyu, game da tattalin arziki da manyan tsare-tsare, da shawarwarin da suka shafi mu'amalar al'adu, da na kwamitin kasuwanci da cinikayya, don karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da mu'amalar al'adu, da aikin soji, da makamashi a tsakaninsu, matakin da zai taimaka wajen inganta shawarwari, da hadin gwiwa game da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.

A nasa bangare, Kerry ya bayyana cewa, kasar Amurka na dora muhimmanci sosai game da sabuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma a matsayin manyan jiga-jigan tattalin arziki biyu a duniya, ya kamata kasashen Sin da Amurka su inganta hadin gwiwa, da kawar da sabani, don kara ingiza dangantakar bangarorin biyu.

Game da batun sauyin yanayi kuwa, Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai game da kiyaye muhallin halittu, kuma yana fatan hadin gwiwar bangarorin biyu zai kara samun ci gaba. Kerry ya ce, kasar Amurka tana fatan inganta mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin, a fannin warware batun sauyin yanayi a duniya.

Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi game da batun zirin Koriya ta Arewa, inda Shugaban Xi ya bayyana matsayin da Sin ke kai game da batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China