in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin da uwar gidansa sun gana da uwar gidan shugaban Amurka
2014-03-22 16:37:44 cri
A daren jiya Jumma'a 21 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwar gidansa, madam Peng Liyuan sun gana da uwar gidan shugaban kasar Amurka, Michelle Obama a Otel na Diaoyutai dake birnin Beijing na Sin.

Shugaba Xi ya yi maraba da zuwan madam Michelle da mahaifiyarta da kuma diyarta, da fatan za ta isar da gaisuwarsa da fatan alheri ga takwaransa Barack Obama.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, dangantaka tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci kwarai ga kasashen biyu da ma duniya baki daya. Yana darajanta dangantakar aiki mai kyau da zumunci tsakaninsa da shugaba Obama. Kuma yana sanya ran sake ganawa da shugaba Obama a Hague dake Holland bayan kwanaki kadan. Kuma yana maraba da cewa, shugaban Obama zai halarci taro da ba a hukunce ba na shugabannin kungiyar APEC a watan Nuwamban bana. Xi ya yi imani cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, dangantaka tsakanin kasashen biyu za ta ci gba da bunkasa zuwa wani sabon mataki.

A nata bangare, madam Michelle ta isar da gaisuwar Barack Obama ga shugaba Xi. Ta ce, ita kanta da mahaifiyarta da kuma diyarta sun damar kawo ziyara a wata kasar waje tare, kuma tana alfahari bisa sakamakon kawo ziyara a Sin. Duk iyalanta suna godiya da goron gayyatar shugaba Xi da uwar gidansa. Ranar 21 ga wata, rana ce ta farko da suka kawo ziyara a Sin, sun samu damar yin mu'amala da dalibai matasan kasar Sin, tare da kai ziyara a babbar fadar sarakunan Beijing. Dukkansu sun burge su sosai. Tana fatan a nan gaba za ta samu karin dama domin kawo ziyara a Sin. Ta sa kaimi ga diyarta da matasan Amurka da su kara fahimta wajen samun ilmi dangane da al'adun gargajiya na sauran kasashen duniya. Yanzu mafi yawan yaran Amurka suna koyon Sinanci a Amurka ko dalibta a Sin. Mu'amala tsakanin matasa na da muhimmanci kwarai da gaske ga dangantaka tsakanin Amurka da Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China