Ranar 6 ga wata, kakakin hukumar manzon musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ke yankin Hong Kong ya amsa tambayar manema labaru dangane da ganawar da ke tsakanin mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da 'yan hamayyar yankin Hong Kong a fadar gwamnatin Amurka wato White House, da kuma sharhin da jaridar New York Times ta Amurka ta bayar, inda ta ce, gwamnatin Sin ta tsoma baki kan babban zaben Hong Kong da ikon watsa labaru cikin 'yancin kai, lamarin da ya lahanci dimokuradiyya da 'yancin kai.
Kakakin ya nuna cewa, a cikin shekaru 17 da suka wuce bayan da aka maido da yankin Hong Kong a karkashin shugabancin kasar Sin, an samu nasarar gudanar da manufar "kasa daya amma tsarin mulkin biyu" a yankin. Bunkasuwar Hong Kong ta fuskar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma harkokin dimokuradiyya ta wuce zaton mutane. Al'ummar Hong Kong sun samu hakkin dimokuradiyya da 'yancin kai da ba su taba samu ba, lamarin da ya samu amincewar kasa da kasa.
Kakakin ya kara da cewa, harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin. Don haka kasar Sin ba za ta yarda da ko wace kasa da ta tsoma baki ko sa hannu kan harkokin cikin gida na Hong Kong ta ko wace hanya ba. Yanzu Hong Kong ta shiga wani muhimmin lokaci a fannin yin gyare-gyare kan harkokin siyasa. Don haka kasar Sin na fatan Amurka za ta yi taka tsan-tsan, a kokarin hana batun Hong Kong ya kawo illa ga dangantakar da ke tsakaninta da Sin. (Tasallah)