in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uwar gidan shugaban Sin da Uwar gidan shugaban Amurka sun kai ziyara a wata makarantar midil a birnin Beijing
2014-03-21 20:50:09 cri
A yau Jumma'a 21 ga wata, Uwar gidan shugaban kasar Sin, Peng Liyuan, da Uwar gidan shugaban kasar Amurka, Michelle Obama sun kai ziyara a makarantar midil ta biyu ta jami'ar horar da malamai ta birnin Beijing.

A lokacin ziyarar Madam Peng Liyuan ta bayyana cewa, al'adu da tarbiyyar Sin da ta Amurka suna da alamar na musamman wanda a ciki ana iya samun darasi daga wajensu don haka tana fatan Madam Michelle Obama da iyalanta za su fahimci dogon tarihi na Sin da ci gaba da aka samu na zamani.

A nata bangare, Mrs Michelle ta bayyana cewa, ziyarar ta a wannan rana ya burge ta da Iyalanta sosai. Ta kuma yi fatan matasan Amurka da na Sin za su kara yin mu'amala a tsakaninsu a nan gaba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China