A lokacin ganawar Mr Li ya nuna cewa, samun dangantaka mai kyau tsakanin Sin da Amurka zai kawo amfani ga kasashen biyu har ma ga daukacin duniya, abin da zai taimaka wajen sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya da kiyaye zaman lafiya da karko a duniya.
Shi ma mataimakin firaministan na Sin Mr Wang Yang ya gana da Jacob Lew tare da yin shawarwari. (Amina)