in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya kai ziyara tawagar likitocin da kasar Sin ta tura kasar Angola
2014-05-09 15:44:46 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kai ziyara da nuna gaisuwa ga tawagar likitocin da kasar Sin ta tura kasar Angola a ranar 8 ga wata da yamma a Luanda, babban birnin kasar Angola.

Tun daga shekarar 1963, kasar Sin ta fara tura rukunonin likitoci zuwa kasashe masu tasowa, a halin yanzu akwai kasashen Afirka fiye da 40 dake cin gajiyar wannan shiri na kasar Sin. Tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu, sau uku ne kasar Sin ta tura tawagogin likitoci zuwa Angola, rukunin likitocin da Li Keqiang ya kai wa ziyara ta zo daga lardin Sichuan na kasar Sin, ya shafe watanni 5 yana aiki a Angola.

Li ya nuna yabo cewa, ko da yake akwai matsalar harsuna, amma ana iya cudanya da zuciya, kuma zuciya ce za ta iyar gano matsalar jama'a, ta yadda jama'ar kasar za su iya fahimtar zumunci daga jama'ar kasar Sin. Ya ce, likitocin Sin sun nuna fasahohinsu na zamani, suna warkar da jama'ar Angola dake fama da cututtuka, a sa'i daya kuma aikin da suke yi a Angola zai kasance muhimmin abin tarihi gare su. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China