in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya jaddada cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan gine-gine irin na jin dadin zaman rayuwar jama'a a ketare
2014-05-09 15:34:04 cri

A ran 8 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranci taron kara wa juna sani a Luanda, babban birnin kasar Angola, kan ayyukan jin dadin rayuwar jama'a, inda ya saurari ra'ayoyi da shawarwari da kamfannonin kasar Sin da Sinawa da ke Angola suka gabatar wajen gudanar da ayyukan jin dadin rayuwar jama'a a kasashen ketare.

Li ya ce, yayin da kamfanonin kasar Sin da Sinawa suke neman bunkasuwa a ketare, ya kamata su rika ra'ayin samun moriya da nasarori tare, ta hakan ne kawai za a iyar samun kyakkyawan sakamako bisa manufar bude kofa ga duniya. Ya kamata a hada ayyukan da muke gudanarwa a ketare tare da la'akari da zaman rayuwar jama'ar wurin, ya kamata kamfanonin kasar Sin da Sinawa su rika bin dokokin wurin, su girmama al'adu da gargajiyar wurin, tare da daukar nauyin da ke bisa wuyansu, da kiyaye kyakkyawar sigar kasar Sin, da nema zaman jituwa a wadannan kasashe ta yadda za su iya kansancewa a matsayin wakilan sada zumunci a tsakanin Sin da kasashen waje. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China