Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bukaci kasarsa da Afrika da su zaburar da dangantakar kafofin watsa labarai tsakaninsu.
A yayin da firaministan na kasar Sin ya kai ziyara a ofishin gidan talabijin na kasar Sin CCTV, wanda ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya, ya bayyana cewar, kafofin yada labarai na kasar Sin da na Afrika su dinga bayar da rahotanni a kan kasashe masu tasowa ta hanyar amfani da fadar gaskiya, tare da yin adalci wajen bayar da rahotanni, ta yadda za'a dinga baiwa kasashe masu tasowa damar sauraren ra'ayoyin su a duniya.
Li, ya baiwa kafofin yada labarai na kasar Sin, kwarin gwiwa wajen yawaita tsara shirye-shirye masu tsananin inganci domin duniya ta fahimci kasar Sin da Afrika. (Suwaiba)