Li Keqiang ya yi nuni da cewa, daddale yarjejeniyar gina wannan hanya ta kasance wani mafari mai kyau, kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da Kenya, domin ganin wannan hanyar wadda ba wai kawai ta sa kaimi ga zirga-zirga a karamin yankin da ke gabashin Afirka ba ne, har ma ta kasance wani abin koyi, a fannin raya zirga-zirgar hanyoyi daban daban a gabashin Afirka.
Li ya kara da cewa, Sin da Afirka suna iya taimakon juna a fannin tattalin arziki, su zama dama ga juna, kuma za su iya samun bunkasuwa tare. Haka a cewarsa baya ga samar da moriya ga jama'arsu fiye da biliyan 2 kai tsaye, zai canza halin da ake ciki bangarori daban daban na bunkasuwar duniya baki daya.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni sun gabatar da jawabai yayin wannan zama. A cikin jawabansu, sun yi nuni da cewa, hanyar da ke hada Mombasa da Nairobi tana da ma'ana mai muhimmanci matuka ga zirga-zirgar gabashin Afirka, da raya karamin yankinsu bai daya. Kazalika sun bayyana cewa, kasashen Afirka suna kasar Sin, wadda ta zama daidaitacciyar abokiya, sahihiya, kuma mai imani, wadda za ta taimakawa kasashen Afirka wajen cimma babban burinsu na raya kasa, da samar da moriya ga jama'arsu. (Danladi)