in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Angola sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi daban-daban
2014-05-09 21:20:35 cri
Yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tattaunawa da shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos a ci gaba da rangadin aikin da ya ke yi a kasar ta Angola, inda ya yi kiran da a kara kokari don kare yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma.

Bangarorin biyu dai sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suka shafi takardun iznin shiga kasa,kiwon lafiya,sha'anin kudi da samar da rance, duk a kokarin da sassan biyu ke yi na bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

Sauran sassan sun hada da aikin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, aikin gona, musayar fasahohin zamani da sauransu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China