in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya dawo gida bayan ziyarar aiki a Afirka
2014-05-12 10:51:28 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya dawo nan kasar Sin a safiyar Litinin din nan, bayan ziyarar aiki da ya gudanar a Habasha, da Najeriya, da Angola da kuma kasar Kenya.

Yayin ziyarsa a Habasha, Mr. Li ya halarci helkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU dake birnin Addis Ababan kasar ta Habasha. Ya kuma halarci taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar kan Afirka a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Wannan ziyara dai da firaministan kasar Sin ya gudanar a nahiyar ta Afirka, ita ce ta farko tun bayan da ya dare mukaminsa a shekarar 2013 da ta gabata, ya kuma gudanar da ziyarar ne tare da uwargidansa Madam Cheng Hong. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China