in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya sauka Nairobi
2014-05-10 17:55:46 cri

Ranar Jumma'a 9 ga wata da dare agogon Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sauka a filin jirgin sama na Kenyatta da ke Nairobi, ya fara ziyarar aikinsa a kasar bisa gayyatar da shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya yi masa. Shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto da kusoshin gwamnatin kasar sun yi maraba ga mista Li da kuma uwar gidansa madam Cheng Hong a filin jirgin saman.

A filin jirgin saman, mista Li ya nuna kyakkyawan fata kan yin musayar ra'ayi tare da shugabannin Kenya kan al'amuran da ke shafar kasashen 2 da kuma wadanda ke jawo hankalin kasashen 2, a kokarin kyautata yin zaman daidai wa daida da amincewa da juna a tsakanin Sin da Kenya da samun moriyar juna da nasara tare, hakan zai kara raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni.

A yayin ziyararsa a Kenya, firaministan kasar Sin zai yi shawarwari da shugabannin kasar, zai kuma tuntubi mutane daga sassa daban daban na kasar, a kokarin bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni, sa'an nan zai gana da manyan jami'an hukumomin MDD da ke Nairobi. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China