Li ya bayyana cewa, Angola ta kasance wata muhimmiyar kasa dake wakilcin Afirka wajen samun saurin bunkasuwa, haka kuma ta zama wata muhimmiyar abokiyar hadin kai ta kasar Sin dake kudu maso yammacin Afirka. Firaministan Sin yana sa ran alheri wajen musanyar ra'ayoyi tare da shugabannin Angola kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sauran batutuwan da ke jawo hankulansu, kuma yana fatan bangarorin biyu su habaka fannonin da suka fi bada hadin gwiwa, da kara samar da karfin bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu.
Mista Li ya isa birnin Luanda ne bayan da ya kai ziyara a Nijeriya cikin nasara tare da halartar taron koli na Afirka na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya karo na 24. (Danladi)