Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na goyon bayan kamfanonin kasar Sin masu inganci da kwarewa da su shiga kasar Angola don zuba jari, kuma wadannan kamfanonin kasar Sin za su ba da taimako wajen bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al'ummar Angola, da kuma samar da karin guraben aikin yi a kasar, sa'an nan kuma, ana bukatar kamfanonin kasar Sin da ma'aikatansu da su kiyaye dokokin kasar da kuma girmama al'adun kasar yadda ya kamata.
Shugaban kasar Angola Jose Eduardo Dos Santos ya bayyana cewa, kasar Angola tana son ci gaba da karfafa musaye-musayen dake tsakanin kasashen biyu don karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu kan fannoni daban daban, da kuma ci gaba da samar da yanayin da ya dace ga kamfanoni da jama'ar kasar Sin wajen zuba jari da kuma kyautata ayyukansu a kasar Angola. (Maryam)