Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kai ziyara a makarantar koyar da fasahohin sana'o'i ta hadin gwiwar Sin da Angola a ranar 8 ga wata dake yammacin Luanda, babban birnin kasar Angola tare da rakiyar mataimakin shugaban kasar Manuel Domingos Vicente.
An kafa wannan makaranta bisa hadin gwiwar kasashen biyu, wadda ke bayar da horo kyauta kan fasahohin sana'o'i ga matasan kasar Angola dake fama da talauci masu shekaru 16 zuwa 25 da haihuwa, tare kuma da ba su taimako wajen ci gaba da samun ilmi da neman guraben ayyukan yi. A halin yanzu dai ana koyar da su kan fasahohin wutar lantarki da sarrafa injuna da dai sauransu, wadanda kasar ke bukata cikin gaggawa.
Li ya jaddadawa shugabannin makarantar cewa, makarantar na kokarin horar da matasa masu fama da talauci kyauta. Ya kara da cewa, ya fi kyau da a kafa makarantu a kasashen Afrika, hakan zai taka rawa wajen mu'ammalar al'adu a tsakanin Sin da kasashen Afrika. (Danladi)