Yayin ganawar da suka yi a safiyar ranar Lahadi, firaminista Li ya furta cewa, kasar Sin za ta ci gaba da marawa Kenya baya a kokarinta na neman samun zaman karko, da bunkasar tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'arta.
Kaza lika Sin za ta hada kai tare da Kenya wajen aiwatar da kudurorin da aka cimma yayin wannan ziyara ta Mr. Li, a kokarin ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni gaba.
A nasa bangare Mr. Ruto ya ce, Kenya na fatan ci gaba da kokari tare da kasar Sin, wajen aiwatar da manufofin da aka cimma a ziyarar, tare da inganta hadin gwiwarsu a fannonin samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da bunkasa harkar noma, baya ga batun inganta harkar yawon shakatawa, da kuma karfafa shawarwari a tsakaninsu kan muhimman lamura na shiyya-shiyya, domin kara azamar fadada dangantaka tsakanin kasashen biyu.(Kande Gao)