A yayin shawarwarin, Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Kenya, ko da yake an samu sauye-sauye sosai a duniya, amma huldar dake tsakanin kasashen biyu tana samun ci gaba kamar yadda ake fata. A yayin da shugaba Kenyatta ya kawo ziyara kasar Sin, shi da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sun daga huldar dake tsakanin kasashen biyu bisa tushen huldar abokantaka irin ta hadin gwiwa, zaman daidai wadaida, amincewa da juna da moriyar juna. Bangaren Sin yana son karfafa yin mu'amala tsakanin kusoshin kasashen biyu, amincewa da juna ta fuskar siyasa, kuma nunawa juna goyon baya kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu.
A nasa bangaren, Mr. Kenyatta ya nuna godiya ga kasar Sin da ta nuna goyon baya ga kokarin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma da kare yanayin halittu da namun daji da kasar Kenya ke yi. Kuma ya ce, ya yarda da matakan da Mr. Li Keqiang ya gabatar a cikin jawaban da ya yi a hedkwatar AU da taron dandalin tattalin arzikin kasa da kasa kan Afirka kwanan baya. (Sanusi Chen)