in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kenya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gina layin dogo
2014-05-12 09:31:18 cri

Firaminstan kasar Sin Li Keqiang da shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya, ta hadin gwiwar gina layin dogo da zai hade biranen Nairobo da Mombasa, a wani mataki na bunkasa harkokin cinikayya da ke yankin gabashin Afirka.

Bikin sanya hannun da ya gudana a ranar Lahadi ya samu halartar shuwagabannin kasashen Uganda, da Rwanda, da na Sudan ta Kudu, baya ga wakilan kasashen Tanzania, da Burundi da kuma jam'an bankin ci gaban Afirka.

Da yake tsokaci yayin sanya hannu kan wannan yarjejeniya, firaminista Li, ya ce, halartar wannan lamari da shuwagabannin kasashen Afirka suka yi ya nuna yadda kasashen gabashin nahiyar ke baiwa harkar sufurin jiragen kasa muhimmanci.

Mr. Li ya kara da cewa, dole ne ko wace kasa ta bunkasa wannan sashe, kafin ta samu damar bunkasa tattalin arzikinta yadda ya kamata. Daga nan sai ya bayyana aniyar kasarsa ta hada kai da daukacin masu ruwa da tsaki wajen habaka sashen gini, da samar da kayan aiki, lura tare da horas da ma'aikatan sufurin jiragen na kasa. Yana mai cewa, hade sassan gabashi, da ma na sauran kasashen Afirka waje guda zai taimaka matuka, wajen fadada tattatalin arzikin nahiyar baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China