in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya ziyarci kungiyar matasa masu aikin ba da hidima ta Kenya
2014-05-12 10:02:37 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ziyarci kungiyar matasa masu aikin ba da hadima ta kasar Kenya a safiyar ranar Lahadi 11 ga wata.

Firaminista Li da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, sun kalli fasahohin da kungiyar ta nuna musu kan allo, tare da sauraron bayani kan yadda kungiyar ke gudanar da aikinta, da kuma habaka cigaban hadin kai a tsakanin Sin da Kenya.

Masu kulawa da aikin na Sin da Kenya sun furta cewa, ta hanyar karfafa horaswa, dukkanin matasa 'yan kungiyar sun kammala kwasa-kwasansu, kafin daga bisani su samu guraban aikin yi.

Game da hakan Li Keqiang ya yaba da wannan aiki, wanda a cewarsa ya kago wani sabon salo na hadin kan kasashen biyu, wanda baya ga bayyana fifikon da kasar Sin ta nuna a fannonin na'urori da fasahohi, ya kuma sa kaimi ga samar da guraban aikin yi a kasar ta Kenya, don haka ya ce ya kamata a yada irin wannan salon a sauran kasashen Afirka.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China