Rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin ya bayyana burin jama'ar kasar 2018-03-21 Mataimakin darektan ofishin nazarin manufofin kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Han Wenxiu ya bayyana a jiya cewa, an yi gyare-gyare guda 86 a cikin rahoton ayyukan gwamnati da aka dudduba da kuma aka zartas a yayin zama na farko na babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, wanda ya shigar da shawarwari daga wakilan jama'ar da kuma 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Rahoton ya bayyana burin jama'ar kasar, yana kuma taimakawa wajen kara cimma daidaito da kara azama kan gudanar da ayyuka. Mista Han ya kara da cewa, a bana kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan neman ci gaba ba tare da tangarda ba, da sa kaimi kan kyautata raya kasar... |
Xi Jinping ya jaddada cewa, ba wanda zai hana ci gaban al'ummar kasar Sin 2018-03-20 A safiyar yau Talata, aka rufe zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a birnin Beijing, inda shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi a karon farko tun bayan da ya sake lashe zaben shugabancin kasar ta Sin... |
Wakilan jama'ar kasar Sin: Sabunta fasahohi shi ne tushen raya masana'antu 2018-03-19 |
Taruka biyu na kasar Sin 2018-03-17 Majalisar wakilan jama'ar kasa hukumar koli ce ta kasa, tana kunshe da wakilan da aka zaba daga larduna, da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu, da birane, da jihohin musamman da rundunar soja. Duk wani dan kasar Sin ko 'yar kasar, in dai shekarunsa ya cika 18 da haihuwa, to, yana da ikon zabar 'yan majalisar da kuma ikon a zabe shi. |
Mambobin CPPCC masu nakasa sun gabatar da shawarwari kan ci gaban kasa 2018-03-16 A jiya da safe, aka kammala taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13 a nan birnin Beijing, yayin taron, wasu mambobin majalisar masu nakasa suka gabatar da shawarwari game da yadda za a raya kasa a madadin daukacin nakasassu dake fadin kasar. |
Daftarin dokar sanya ido zai samar da tabbaci ga tafiyar da harkokin kasa bisa doka, in ji 'yan majalisar NPC 2018-03-15 A ranar 13 ga wata ne aka gabatar da daftarin dokar sanya ido ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) da ke gudana a nan birnin Beijing don a dudduba shi, dokar wadda ke da nufin karfafa gyare-gyaren tsarin sa ido na kasar Sin ta fannin dokoki, tare kuma da yaki da cin hanci da rashawa bisa dokokin da aka samar. 'Yan majalisar da suka halarci taron sun bayyana cewa, dokar za ta taimaka ga kafa tsarin sanya ido mai inganci, wadda kuma ta nuna niyyar jam'iyyar kwaminis mai mulki ta kasar ta fannin yaki da cin hanci da rashawa. |
An mika shirin gyaran fuskar tsarin gwamnatin kasar Sin ga majalisar kasar domin a tantance shi 2018-03-14 |
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi bayani kan ayyukan da ta yi na kafa dokoki da sa ido 2018-03-13 An shirya taron manema labaru game da zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a Jiya Liitinin, inda wasu jami'an hukumomin majalisar suka amsa tambayoyin 'yan jarida kan batutuwan da suka shafi kafa dokoki da sa ido. |
An zartas da gyaran kundin tsarin mulkin kasar Sin bisa yawan kuri'un da aka kada 2018-03-12 An zartas da gyaran kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a yayin zaman taro na 3,na zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar karo na 13 da aka shirya jiya Lahadi a nan birnin Beijing. Haka zalika, an kara shigar da sabbin abubuwan cikin kundin wanda ya shafi gudanar da harkokin kasar Sin a sabon zamani bayan shekaru 14. |
Gyaran kundin tsarin mulkin kasar Sin shi ne muhimmin matakin sa kaimi wajen inganta karfin sarrafa kasar 2018-03-10 |
Xi Jinping: dole ne a aiwatar da manyan tsare-tsaren bunkasa yankunan karkara 2018-03-09 Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar Mr. Xi Jinping, ya ce aiwatar da manyan tsare-tsaren raya yankunan karkara, muhimmin aiki ne da JKS ta kaddamar a yayin babban taron wakilanta karo na 19, sannan babban aiki ne da ke kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni da kafa kasa ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni... |
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi bayani kan manufar kasar a fannin diplomasiyya 2018-03-08 A yau Alhamis ne aka kira wani taron manema labaru a yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi bayani kan burin da kasar ta sanya a gaba a kokarinta na inganta hulda da kasashen waje, da makomar shawarar "ziri daya da hanya daya", da yanayin da kasar Sin ke ciki a fannin harkar diplomasiyya, da dai sauransu. |
Masanin Najeriya: Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai taimakawa kasashen nahiyar Afirka nesa ba kusa ba 2018-03-08 A cikin rahoton aikin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayar a yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na bana, ya bayyana cewa, cikin shekaru biyar da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu babban ci gaba, kason da tattalin arzikin kasar ke dauka cikin gaba dayan tattalin arzikin duniya ya karu daga kashi 11.4% zuwa kimanin kashi 15%, kuma yawan gudummawar da kasar ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya zarce kashi 30%... |
Xi Jinping na fatan yankin Mongolia na gida zai yi kokarin raya tattalin arziki mai inganci tare da kawar da talauci daga yankin 2018-03-06 Da yammacin jiya Litinin 5 ga watan Maris, wato ranar da aka kaddamar da zagayen farko na babban taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya halarci taron tattaunawa kan rahoton aikin gwamnati da aka gabatar wanda kungiyar wakilan yankin Mongolia na gida ya shirya, inda Xi Jinping ya ba da shawarar raya yankin Mongolia na gida, tare da neman jami'ai da al'ummomin yankin su yi namijin kokari da kuma kara hada kan kabilu daban daban domin bunkasa tattalin arziki mai inganci, da samun sakamako na a zo a gani wajen kawar da talauci daga yankin. Bugu da kari, yana fatan kabilu daban daban da suke zaune a yankin, za su kara hada kai domin tabbatar da tsaron yankin dake kan iyakar kasa da kasa dake arewacin kasar Sin... |
An bude taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin 2018-03-05 Taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na wannan karo, yana tare da nauyin sauya fasalin gwamnatin kasar bayan wa'adin ta na shekaru 5 ya cika. Saboda haka, firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya waiwayi ayyukan da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru 5 da suka gabata. Inda ya ce, a wadannan shekaru, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba sosai, kana kudin kayayyakin da take samarwa a gida a ko wace shekara,ya karu daga kudin Sin Yuan biliyan 54000 zuwa biliyan 82700, wanda ya kai kashi 30% na ci gaban tattalin arzikin daukacin kasashen duniya. Ban da wannan kuma, kasar tana kan gaba a duniya, a fannonin shimfida layin dogo ga jirgin kasa mai gudun gaske, da cinikayya ta hanyar kafar Internet, da biyan kudi ta wayar salula, da dai makamantansu. An ce, zuwa yanzu tsawon layin dogo na jirgin kasa mai gudun gaske da aka shimfida a kasar ya karu daga kilomita fiye da 9000 zuwa 25000, wanda tsawonsu ya kai kashi 2 bisa kashi 3 na tsawon dukkanin layin dogon jirgin kasa mai gudun gaske da aka gina a duniya. Sa'an nan yawan al'ummar kasar masu fama da talauci ya ragu da fiye da miliyan 68, kuma yawan matalauta bisa daukacin al'ummar kasar ya ragu daga kashi 10.2% zuwa kashi 3.1%. Haka zalika, muhallin halittu na kasar na kara samun kyautatuwa, yayin da yawan ranekun da wasu birane suke fama da gurbatacciyar iska ya ragu zuwa rabin adadin da aka samu a baya... |