180320-xijinping-maryam.m4a
|
Cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, zai ci gaba da aiwatar da ayyukan da kudin tsarin mulkin kasar Sin ya dora masa, yayin da kiyaye al'ummar kasa cikin himma da kwazo, haka kuma, ya yi amanna cewa, babu wanda zai iya hana ci gaban al'ummar kasar Sin bisa hadin gwiwarmu baki daya.
"A matsayi na shugaban kasar Sin, ina alfahari kwarai da gaske, kuma ina sane da muhimman nauyin dake gabana. Zan ci gaba da aiwatar da ayyukana kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar Sin ya bukaci shugaban kasar Sin, zan dukufa wajen bautawa kasata, da al'ummar kasar baki daya, a yayin gudanar da ayyuka cikin himma da kwazo yadda ya kamata. Haka kuma, ina maraba da sa idon da al'ummar kasa za su yi mini, domin cimma alkawarin da na yiwa jama'ar kasar Sin baki daya."
Xi Jinping ya yi wannan alkawari ne a gaban wakilan al'ummar kasar Sin su kimanin dubu 3, a bikin rufe zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13.
Haka kuma, shugaba Xi ya sha ambaci kalmar "al'umma" a yayin da yake jawabi, domin ya ma bukaci ma'aikatan hukumomin gwamnatin kasar Sin da su sanya al'ummar kasar a matsayin farko a cikin zukatansu, domin bautawa al'ummar kasar yadda ya kamata, da kuma gudanar da ayyukansu bisa babban burin tallafawa al'ummar kasa baki daya.
A sa'i daya kuma, shugaba Xi Jinping ya maimaita tarihin ci gaban kasar Sin baki daya cikin jawabinsa, yana mai cewa: "Sinawa su kan ce, komai nisan hanya, in mu ci gaba da yin tafiya, tabbas ne za mu isa. Tun lokacin da aka shiga tsakiyar karni na 19, mutanen kasar Sin sun dukufa wajen neman ci gaba cikin hadin gwiwa, duk da irin dimbin kalubalolin da suka gamu da su cikin shekaru sama da 170 da suka gabata. Shi ya sa, ya zuwa yanzu, muna zaman mafi kusa da burinmu na farfadowar kasa, a nan gaba kuma, idan al'ummar kasar kimanin biliyan 1.3 muka ci gaba da dukufa cikin hadin gwiwa, tabbas ne za mu cimma burinmu na neman farfadowar kasar baki daya."
Bugu da kari, shugaba Xi ya jaddada cewa, dukkanin ikon kasa su ne na al'ummar kasa. In al'umma suna da imani, sai kasa ta samu karfi, za ta samu makoma mai haske.
"Ya kamata a yi bincike kan ko muna gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, ko a'a, ko al'ummar kasa sun amince da ayyukan, ko suna goyon bayan ayyukan, kuma ko sun gamsu da sakamakon da aka samu. Kuma ya kamata a maida hankali kan batutuwan da suka fi janyo hankulan al'ummar kasa, domin za su ji dadi da yin alfahari cikin hanyarmu ta neman farfadowar kasa a nan gaba."
A yayin taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 19, an tsara shirye-shiryen gina zamantakewar al'umma mai wadata a fadin kasar Sin baki daya, fara ayyukan gina sabuwar kasa ta zamani karkashin tsarin gurguzu bisa dukkan fannoni, da kuma cimma burin neman farfadowar kasa. Shugaba Xi ya ce, ya kamata a dukufa ba tare da kasala ba ko kadan domin aiwatar da shirye-shiryen yadda ya kamata.
Kana, ya kamata a karfafa yin kwaskwarima a kasar, da bude kofa ga waje, sa'an nan a raya harkokin dimokuradiyya bisa tsarin gurguzu, domin inganta tsarin gudanarwar ayyukan kasa na zamani, yayin da ake gaggauta gina zaman al'umma mai karfi karkashin tsarin gurguzu.
Haka zalika, ya kamata a ci gaba da ayyukan kawar da talauci da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma baki daya, domin ciyar da yanayin adalci a kasar Sin gaba. A sa'i daya kuma, za a tsaya tsayin daka kan jagorancin JKS kan sojojin al'ummar kasar Sin, yayin da za'a gaggauta ayyukan gina karfin soja dake kan gaba cikin kasa da kasa.
Bugu da kari, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da manufofin masu cin gashin kansu da suka hada da "Kasa daya, tsarin mulki iri biyu", "Mutanen HongKong su kula da harkokin HongKong" da kuma "Mutanen Macao su kula da harkokin Macao" yadda ya kamata, yayin tsayawa tsayin daka kan manufar "kasa daya tak" da kuma matsaya daya da aka cimma kan dinkuwar kasar Sin baki daya a shekarar 1992 a yankin Taiwan, domin inganta dunkulewar kasar Sin cikin zaman lafiya.
Xi Jinping ya ce: "Kare ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasar, da kuma samun dunkulewar kasa baki daya su ne fatan al'umma, da kuma moriyar al'umma. Duk wanda yake da aniyar raba kasa, zai samu zargi daga dukkanin al'umma, da kuma hukuncin da tarihi zai yanka masa! Al'ummar kasar Sin suna da aniya da imani mai karfi wajen yaki da dukkan aikace-aikace masu haddasa rabuwar kasa! Kuma dukkan al'ummomin kasa suna da aniyar kiyaye cikakken zaman kasar ta Sin, babu wanda zai iya raba yanki ko daya daga kasar Sin!" (Maryam Yang)