in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi bayani kan ayyukan da ta yi na kafa dokoki da sa ido
2018-03-13 13:15:31 cri

An shirya taron manema labaru game da zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a Jiya Liitinin, inda wasu jami'an hukumomin majalisar suka amsa tambayoyin 'yan jarida kan batutuwan da suka shafi kafa dokoki da sa ido.

Ana iya ganin cewa, tun da aka shiga yanayin sanyi a bara, yanayin hazo da a kan samu a arewacin kasar Sin ya ragu. A yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya, an kara ambatar batun kafa dokoki don rigakafi da kuma shawo kan matsalar gurbatar muhalli. Game da haka, mambar kwamitin kiyaye muhalli da albarkatu na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin madam Lv Caixia ta bayyana cewa, a fannin inganta ayyukan kiyaye muhallin halittu, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 ya kafa dokoki bisa tushen kiyaye moriyar jama'a, kana ta jaddada tare da warware hakikanan matsalolin da suka shafi gurbatar yanayi da ruwa bisa yanayin da kasar Sin ke ciki. Lv Caixia ta ce,

"Ga misali, mun gyara dokar kiyaye muhalli da dokar kiyaye namun daji da dokar kiyaye muhallin teku da dokar yanayi da rigakafi da shawo kan gurbatar muhalli da kuma dokar yin rigakafi da shawo kan gurbatar ruwa. kana mun tsara dokar bincike da habaka albarkatun dake yankin karkashin teku mai zurfi da dokar tsaron makamashin nukiliya da kuma dokar yin rigakafi da shawo kan gurbatar kasa da har yanzu ake duddubawa da dai sauransu. Baya ga haka, muna mayar da hankali sosai kan bukatun jama'a ta fuskar iska mai tsabta da ingancin ruwan sha, don haka mun kara kyautata dokokin da suka shafi kiyaye muhalli, da yin rigakafi da shawo kan gurbatar yanayi da ruwa da dai sauransu, kana mun karfafa karfin hukunta ayyukan da suka sabawa dokokin."

Ban da yin gyare-gyare masu tsanani kan wasu dokoki, kwamitin kiyaye muhalli da albarkatu na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na karfafa ayyukan sa ido ta hanyoyi daban daban, ciki har da yin bincike na musamman a cikin shekaru 5 da suka wuce. Game da hakan, mataimakin daraktan kwamitin mista Yuan Si ya ce,

"A hakika dai, zaunannen kwamitin majalisar da kwamitin kiyaye muhalli da albarkatu suna gudanar da ayyukan sa ido kan rigakafi da shawo kan gurbatar yanayi kamar yadda ake buga kusa, wato ana ta aiki har zuwa lokacin da aka samu sakamako mai kyau. Wannan ita ce bukatarmu. Ta hanyar yin bincike da nazari har na tsawon shekaru 5, mun inganta tabbatar da wasu muhimman tsare-tsare, ciki har da neman ci gaban biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei yadda ya kamata, tare da yin rigakafi da shawo kan gurbatar yanayi da dai sauransu."

A yayin da aka waiwayi ayyukan kafa dokoki a cikin shekaru 5 da suka wuce, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya bayyana a kwanan baya cewa, an kafa wasu dokoki da dama masu amfani cikin sauri, ana iya cewa, tsarin dokoki na gurguzu mai hayalayyar musamman ta kasar Sin dake dora muhimmanci kan kundin tsarin mulki ya kara samun kyautatuwa da ci gaba. Baya ga haka, an zartas da manyan tanade-tanaden da suka shafi harkokin jama'a, wanda ya aza harsashi mai kyau wajen rubuta dokar da ta shafi harkokin jama'a mai halin musamman na kasar Sin, wadda kuma ke iya nuna ra'ayin jama'a.

Mataimakin daraktan kwamitin kula da ayyukan dokokin shari'a na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin mista Wang Chaoying ya bayyana a jiyan cewa, bayan zartas da tanade-tanaden da suka shafi harkokin jama'a, yanzu haka ana jera dokokin da suka shafi wannan fannin yadda ya kamata. Wang Chaoying ya kara da cewa,

"Bisa shiri na farko, za a tsara wasu sassan da suka shafi mallakar dukiyoyi da kwantaragi da alhakin karya dokar ikon mallaka da aure da iyali, da kuma gado da dai sauransu. Bisa lokacin da aka tsaida, za a gabatar da sassan baki daya ga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a don yin nazari kansa a karshen shekarar da muke ciki, daga baya kuma, za a dudduba sassan dokoki daya bayan daya, ana kokarin ganin an zartas da su ya zuwa shekarar 2020, idan an hada kan su da tanade-tanaden, za su bullo da hadaddiyar dokar da ta shafi harkokin jama'a." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China