180315-daftarin-dokar-sanya-ido-zai-samar-da-tabbaci-ga-tafiyar-da-harkokin-kasa-bisa-doka-lubabatu.m4a
|
A ranar 13 ga wata ne aka gabatar da daftarin dokar sanya ido ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) da ke gudana a nan birnin Beijing don a dudduba shi, dokar wadda ke da nufin karfafa gyare-gyaren tsarin sa ido na kasar Sin ta fannin dokoki, tare kuma da yaki da cin hanci da rashawa bisa dokokin da aka samar. 'Yan majalisar da suka halarci taron sun bayyana cewa, dokar za ta taimaka ga kafa tsarin sanya ido mai inganci, wadda kuma ta nuna niyyar jam'iyyar kwaminis mai mulki ta kasar ta fannin yaki da cin hanci da rashawa.
Dokar sanya ido da aka gabatar ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta tanadi ayyukan da ya kamata hukumomin sanya ido su gudanar, da ikon da suke da shi, da kuma yadda za a sanya musu ido daga wasu fannoni bakwai, kuma 'yan majalisar mahalarta taron sun bayyana ra'ayoyinsu a kan dokar kamar haka, "Akwai abubuwa na a zo a gani da dama a game da dokar. A da an sanya ido a kan jami'an jam'iyyar kwaminis ta kasar, da kuma jami'an gwamnati ne kawai, amma dokar da aka gabatar ta shafi dukkanin sassan da ke gudana bisa ikon da al'umma suka ba su, ciki har da kamfanoni da hukumomin al'umma." "Dokar ta mai da ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a kan hanyar doka, ta kuma tara sassan yaki da cin hanci da ake da su a gu daya. Dokar da aka samar za ta taimaka ga sanya ido a kan hukumomin da ke tafiyar da ikon al'umma."
A yayin da 'yan majalisar suke dudduba daftarin dokar, 'yan majalisar mahalarta taron sun ce, zurfafa gyare-gyaren tsarin sanya ido muhimmin gyara ne da jam'iyyar kwaminis ta kasar ta gudanar ga tsarin siyasa na kasar. Dan majalisar wanda kuma shi ne magajin garin birnin Karamay na kasar, Mr. Wang Gang ya bayyana cewa, "Daftarin dokar sanya ido ta mai da niyyar jam'iyyar kwaminis ta kasar ta inganta tsarin sanya ido zama dokoki, matakin da kuma ya shaida niyyar jam'iyyar ta kin jurewa ayyukan cin hanci da rashawa."
Har wa yau, 'yan majalisar mahalarta taron suna ganin cewa, dokar sanya ido da aka samar za ta inganta aiwatar da tsarin mulkin kasar, da ma inganta tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar, haka kuma mataki ne na inganta tsarin tafiyar da harkokin kasar. Chen Chunping, dan majalisar wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da harkokin kudi ta jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui ta kasar ya ce, "Dokar sanya ido ta kayyade tsarin sanya ido ta kasar Sin daga bangaren dokoki, wadda kuma ta hada manufar daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar, da manufar tafiyar da harkokin kasa bisa doka, wadda kuma ta hada aikin sanya ido a kan harkokin jam'iyyar da sanya ido a kan hukumomin dake karkashin ikon al'umma, dokar ta kuma inganta tsari da dokoki ta fannin yaki da cin hanci da rashawa."
Har wa yau, Chen Manqi, 'yar majalisar da ta zo daga Hongkong, wadda kuma ita ce shugabar kungiyar kanana da matsakaitan rukunonin lauyoyi ta Hongkong, tana ganin cewa, dokar ta kasance wani muhimmin ci gaba da kasar Sin ta samu, bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekaru 40 da suka wuce, ta ce, "Dokar sanya ido ci gaba ne da muka samu tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekaru 40 da suka wuce, a kokarin da muka yi na kafa tsarin dokoki da yayata manufar tafiyar da harkoki bisa dokoki, da kuma kayyade tsarin sanya ido ta yadda za a kara inganta tsarin dokoki na sanya ido."(Lubabatu)