in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan jama'ar kasar Sin: Sabunta fasahohi shi ne tushen raya masana'antu
2018-03-19 12:57:01 cri

Yayin da taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wasu wakilan jama'a sun sheda wa wakilin CRI cewa, kamata ya yi a yi kokarin sabunta fasahohi don raya masana'antun kasar.

Kamfanin "Jiangsu Sunshine Group" wani kamfani ne dake sana'ar saka gashin tumaki da samar da tufafi. A shekarun baya, kamfanin ya yi amfani da fasahohi masu alaka da yanar gizo ta Internet, wajen samar da tufafin da ya dace da tsarin jikin daidaikun mutane. Ta wannan sabuwar fasaha, kamfanin ya samu nasara sosai yayin da yake takara da sauran kamfanoni. Yayin da ake magana da Madam Chen Lifen, shugabar kamfanin, ta ce idan ana son inganta harkar samar da kaya, dole ne a yi kokarin neman samun ci gaba a fannonin hada sinadarai da samar da kayayyaki, gami da hidima, ta yadda za a samu damar kirkiro sabbin fasahohi, da biyan bukatun jama'a na samun zaman rayuwa mai kyau. A cewarta,

"A bara mun kafa wata sabuwar alamar tufafi domin daliban da suka gama karatun jami'a, sa'an nan mun ba dalibai damar sayar da tufafinmu a cikin jami'o'i. Zuwa yanzu mun kafa kantuna cikin jami'o'i 33 na larduna fiye da 20, inda aka ja hankalin dalibai da yawa, wadanda suka zama ma'aikatanmu. Lamarin ya shaida cewa, idan dai ana kokarin kirkiro sabbin fasahohi da tunani, to, ko tsohuwar sana'a ma ba za a hana ta samun ci gaba ba."

Yayin da kasar Sin ke kokarin aiwatar da manufarta ta "raya kasa ta hanyar kyautata fasahohin masana'antu", wasu manyan kamfanoni na taka rawar gani wajen biyan bukatun gwamnati a wannan fanni, cikin su har da kamfanin samar da motoci na "SAIC Motor". A ganin shugaban kamfanin SAIC Motor, Chen Hong, don raya masana'antu, tilas ne a yi kokarin sabunta fasahohin da ake amfani da su. Inda ya ce,

"Idan mun dauki kamfaninmu a matsayin misali, za ka ga yadda muke rungumar sabbin fasahohi masu alaka da yanar gizo wato Internet. Wannan manufa ta ba mu damar samar da motocin da ke samun karbuwa, da gyara tsarin motoci bisa bukatun jama'a, da samar da ingantattun kayayyakin mota, ta yadda za mu iya ciyar da kamfaninmu gaba. "

An ce, cikin karin motocin da kamfanin SAIC Motor ya samu sayarwa a bara, yawan motocin da kamfanin ya tsara da kansa ya zarce kashi 50%. Hakan ya nuna cewa, motocin da kamfanin ya tsara da kansa, maimakon wasu motocin kirar sauran kamfanoni, sun zama abin da ya fi samar wa kamfanin riba.

Ban da wannan kuma, rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin da aka gabatar wajen taron wakilan jama'ar kasar Sin na wannan karo, ya ambaci bukatar mai da hankali kan alkaluma, da kara yin amfani da na'urori masu kwakwalwa wadanda ke iya gudanar da ayyuka da kansu, wato AI a Turance. Dangane da wannan batu, Sun Pishu, wani wakilin jama'ar kasar Sin, kuma shugaban kamfanin Inspur mai samar da hidimar na'urori masu kwakwalwa, ya ce, don kara raya masana'antun kasar Sin, ya kamata a dora muhimmanci kan dimbin alkaluman da aka samu daga na'urorin sadarwa da kamfuta. A cewarsa,

"Don gudanar da shirinmu na 'raya masana'antu har zuwa shekarar 2025', ya kamata a yi kokarin hada masana'antu da fasahohi masu alaka da alkaluma, da AI, da dai makamantansu, ta yadda za a samu damar yin amfani da alkaluman da aka samu daga fannonin samar da kaya da gudanar da harkokin kamfanoni da saye da sayar da kaya, yadda ya kamata. Za a yi la'akari da alkaluman da aka samu, kafin a fara samar da kaya, ta yadda kayayyakin za su zama masu inganci, da za su iya biyan bukatun daidaikun mutane."

A nasu bangaren, wasu wakilan jama'ar kasar Sin sun ce, nan gaba, dole ne a dauki sabbin fasahohi wajen inganta kayayyakin da ake samarwa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China