in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin CPPCC masu nakasa sun gabatar da shawarwari kan ci gaban kasa
2018-03-16 10:44:25 cri

A jiya da safe, aka kammala taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13 a nan birnin Beijing, yayin taron, wasu mambobin majalisar masu nakasa suka gabatar da shawarwari game da yadda za a raya kasa a madadin daukacin nakasassu dake fadin kasar.

Li Qingzhong, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar wanda ya halarci taro na farko na majalisar ta 13 da aka gudanar a nan birnin Beijing, shi ma nakasashi ne saboda kusan ba ya gani, ya gaya mana cewa, "Ko tafin hannuna ba na gani, ita ma ba ta jin muryata, amma zukatunmu na hade."

Matar da Li Qingzhong ya ambata ita ce Gao Xiaodi, tsohuwar mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wadda take da shekarun haihuwa 63 a bana, kawo yanzu an zabe ta a matsayin mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar har sau uku, yayin taron da aka gudanar, Gao Xiaodi ta yi magana ne tana nuna alama da hannu, haka kuma ta zanta da Li Qingzhong wanda ke fama da matsalar ganin abu da alamar hannu, He Yang mai yiwa nakasassu tafinta, ta ce, "Madam Gao Xiaodi ta ce, nakasassu wadanda ba su iya ganin abu ko jin wani sauti suna fama da wahala a zaman rayuwarsu na yau da kullum, a don haka suna kokari matuka tare domin taimakawa daukacin nakasassu a fadin kasar, a yayin taron majalisar da aka gudanar na shekarar bara, ba a zabi makaho a matsayin mamba domin ya halarci taron ba, amma bana an kara wani a taron, tana ganin cewa, lamarin yana da kyau sosai, saboda hakan zai taimaka wajen kiyaye hakkin nakasassu."

Duk da cewa, nakasassu mambobin majalisar suna fama da wahalhalu a wasu fannoni, amma suna taka muhimmiyar rawa kan aikin ba da shawara game da harkokin siyasa ta kasar Sin, Li Qingzhong, shi ma mamba ne na kungiyar nakasassun kasar Sin kuma zaunannen mataimakin shugaban kungiyar makafi ta kasar Sin, yana ganin cewa, yanzu a kasar Sin, yawancin makafi suna gudanar da aikin tausa, amma suna fatan za su kama wasu sabbin ayyuka kamar sauran mutanen wadanda suke da karfi, yana mai cewa, "Yanzu muna kokarin samar da sabbin ayyuka ga makafi, muna fatan makafi za su iya yin aiki kamar malanta ko aikin lauya ko ma'aikatan hukumomin gwamnati da sauransu, na san a kasashen waje, misali kasashen Turai da kasar Amurka, duk da cewa yana da wuya makafi su samu aikin yi, amma suna gudanar da ayyuka iri daban daban, misali shehun malami a jami'a ko injiniya ko lauya."

Yayin taron tattaunawar da aka shirya da kungiyoyi yayin taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, mambobi mahalarta taron sun yi magana daya bayan baya domin musanyar ra'ayi, madan Gao Xiaodi ita ma ta shiga tattaunawa ta hanyar nuna alamar hannu bisa taimakon mai aikin fassara alamar hannu, jagoran taron Yu Gesheng ya gaya mana cewa, ko shakka babu mamba Gao Xiaodi tana yin kokari matuka, ya ce, "Ko da yake Gao Xiaodi ba ta iya jin muryar sauran mutane, amma har kullum tana kokarin bayyana ra'ayinta bisa taimakon mai aikin fassara alamar hannu, muna iya tattaunawa tsakaninmu babu wata matsala, ko a babban taron, ko a taron tattaunawa da aka shirya tsakanin kungiyoyi, kana daga abun da ta bayyana, an lura cewa, ta shirya sosai kafin ta zo taron, ina ganin cewa, muna cikin wani babban iyali ne, mun halarci taron domin taka rawa kan aikin raya kasarmu."

Ta bakin mataimakinta, Gao Xiaodi ta gaya mana cewa, yawancin batutuwan da ta gabatar ga taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar suna shafar nakasassu ne, kuma abu mai faranta rai shi ne an riga an warware yawancin matsalolin da ta gabatar, har adadin ya kai kusan kaso 90 bisa dari, misali, yanzu adadin Sinawa da ba su ji ya kai sama da miliyan 20, amma yawancin gidajen telebijin a fadin kasar ta Sin ba su samar da hidimar fassara yayin da suke watsa labarai ba, shi ya sa ta gabatar da wannan batu ga taron, yanzu sannu a hankali ana daidaita wannan batu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China