in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Najeriya: Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai taimakawa kasashen nahiyar Afirka nesa ba kusa ba
2018-03-08 11:02:40 cri



A cikin rahoton aikin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayar a yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na bana, ya bayyana cewa, cikin shekaru biyar da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu babban ci gaba, kason da tattalin arzikin kasar ke dauka cikin gaba dayan tattalin arzikin duniya ya karu daga kashi 11.4% zuwa kimanin kashi 15%, kuma yawan gudummawar da kasar ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya zarce kashi 30%.

Game da wannan, Ehizuelen Michael Mitchell Omoruyi, babban daraktan cibiyar binciken harkokin Najeriya dake Jami'ar horas da malamai ta Lardin Zhejiang na kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana tafiya kamar yadda ya kamata kuma yana kara tasiri da ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Haka kuma irin ci gaban zai taimakawa tattalin arzikin kasashen Afirka. Yana mai cewa,

"Hakika ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai taimakawa kasashenmu na nahiyar Afirka nesa ba kusa ba. Idan ka kalli wani rahoto da masanan tattalin arziki suka wallafa a wata mujallar tattalin arziki, ya nuna yadda kasashen Afirka suka amfana sakamakon alakar kasar Sin da kasashen Afirka, wadannan fannonin sun hada da bunkasar harkokin cinikayya tsakanin sassan biyu daga dala biliyan goma a shekarar 2000 zuwa dala biliyan 220,000 a shekarar 2014. Wannan ya faru ne sakamakon yadda bangarorin biyu ke bukatar juna, haka kuma wannan ya taimaka wajen samar da kayayyakin bukatun yau da kullum masu araha ga al'ummomin nahiyar Afirka."

Ban wannan kuma Mr. Ehizuelen yana ganin cewa, kyakkyawar alakar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki ta kawo babban canji a Afirka. Ya kara da cewa,

"Wannan dangantaka tana da fa'ida, dalili kuwa shi ne, kasar Sin ta kawo muhimman sauye-sauye a nahiyar Afirka. Na farko bangaren muhimman kayayyakin more rayuwa, kuma wannan yana da muhimmanci ga nahiyar. A baya-bayan nan ajandar da kungiyar AU ta gabatar game da raya nahiyar nan da shekara 2063 na cewa, idan aka samar da kayayyakin more rayuwa hakan zai taimakawa nahiyar samun karuwar kaso 50 cikin 100 na tattalin arzikinta nan da shekarar 2040. Amma maganar gaskiya ita ce, kasashen Afirka na fama da matsalar kayayyakin more rayuwa, sai dai tun lokacin da kasar Sin ta kulla akala da kasashen Afirka, kasar Sin ta taimakawa nahiyar cin gajiyar albarkatunsu wajen gina muhimman kayayyakin more rayuwa da kasashen na Afirka ke bukata domin cimma burinsu na raya kansu.

Misali a nan ita ce kasar Angola, kasar da ta dogara kwacakwan a kan mai, domin kashi 60 cikin 100 na GDPn kasar ya dogara ne a kan man da kasar take hakowa. Sai dai tun lokacin da kasar Sin ta fara zuba jari a kasar ta Angola bisa taimakon da bankin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin ya bayar, tattalin arzikin kasar ya samu kudaden da suka kai a kalla dala miliyan 600, matakin da ya samar da guraben ayyukan yi da dama a kasar.

Ana kuma hasashen cewa, za a samar da guraben ayyukan yi miliyan 800 a kasashen Afirka sakamakon dangantakar Sin da Afirka, don haka akwai bukatar kasashen Afirka su sake daura damara, don ganin an cimma wannan buri. Haka kuma fatan kasar Sin a alakarta da nahiyar Afrka shi ne taimakawa nahiyar ta bunkasa ta hanyar cin gajiyar albarkatunta ta yadda al'ummomin nahiyar za su samu rayuwa mai inganci kamar kowa ba tare da gindaya wani sharadi ba."

A ganin Mr. Ehizuelen, ba ma kawai kasar Sin ta mai da hankali kan zuba jari a Afirka ba, a'a har ma tana kuma musayar ilimi da Afirka. Ya ce,

"Idan kuma ba a manta ba a taron FOCAC na Afirka ta kudu, kasar Sin ta taimakawa Afirka da dala miliyan 60, baya ga wasu rancen kudaden raya kasa da na Ilimi da ta baiwa kasashen na Afirka. An kuma yi hasashen cewa, nan da shekarar 2060, Afirka za ta fi ko wace kasa yawan al'umma, idan matasan nahiyar ba su da Ilimi ko kwarewar da duniya ke bukata, kasashen Afirka ba za su iya cimma burinsu na bunkasuwa ba. Kasar Sin ta san muhimmancin Ilimi, domin a lokacin da take kokarin raya kanta a baya, kasar Sin ta yi amfani da Ilimi don kaiwa ga matsayin da take a halin yanzu. Wannan ne ya sa kasar Sin ta ke kara baiwa kasashen Afirka guraben karo Ilimi domin su yi karatu a kasar Sin, ta yadda bayan daliban sun kammala karatunsu za su koya su raya kasashensu. Wannan zai baiwa nahiyar damar zama mai samar da guraben ayyukan yi ga matasanta maimakon dogara da wasu kasashe."(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China