180305-an-bude-taron-majalisar-wakilan-jamaar-kasar-sin-bello.m4a
|
Taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na wannan karo, yana tare da nauyin sauya fasalin gwamnatin kasar bayan wa'adin ta na shekaru 5 ya cika. Saboda haka, firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya waiwayi ayyukan da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru 5 da suka gabata. Inda ya ce, a wadannan shekaru, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba sosai, kana kudin kayayyakin da take samarwa a gida a ko wace shekara,ya karu daga kudin Sin Yuan biliyan 54000 zuwa biliyan 82700, wanda ya kai kashi 30% na ci gaban tattalin arzikin daukacin kasashen duniya. Ban da wannan kuma, kasar tana kan gaba a duniya, a fannonin shimfida layin dogo ga jirgin kasa mai gudun gaske, da cinikayya ta hanyar kafar Internet, da biyan kudi ta wayar salula, da dai makamantansu. An ce, zuwa yanzu tsawon layin dogo na jirgin kasa mai gudun gaske da aka shimfida a kasar ya karu daga kilomita fiye da 9000 zuwa 25000, wanda tsawonsu ya kai kashi 2 bisa kashi 3 na tsawon dukkanin layin dogon jirgin kasa mai gudun gaske da aka gina a duniya. Sa'an nan yawan al'ummar kasar masu fama da talauci ya ragu da fiye da miliyan 68, kuma yawan matalauta bisa daukacin al'ummar kasar ya ragu daga kashi 10.2% zuwa kashi 3.1%. Haka zalika, muhallin halittu na kasar na kara samun kyautatuwa, yayin da yawan ranekun da wasu birane suke fama da gurbatacciyar iska ya ragu zuwa rabin adadin da aka samu a baya.
Firaministan kasar Sin ya kara da cewa
"A shekaru 5 da suka wuce, mun tinkari kalubale daban daban, kana wasu abubuwan da suka faru a kasarmu da ma kasashen waje, sun kasance irin wadanda ba a taba gani ba a tarihi, saboda haka ba cikin sauki muka samu nasarorin aiwatar da gyare-gyare da neman ci gaba ba. Wannan shi ne sakamakon da aka samu, karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda shugaba Xi Jinping ke jagoranta."
Har wa yau, cikin wannan rahoton da firaministan kasar Sin ya gabatar, an ambaci wasu burikan da ake neman cimmawa a fannin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin. Ga misali, ana neman ganin an samu karuwar alkaluman kayayyakin da ake samarwa a gida wato GDP da kashi 6.5%, sa'an nan za a shawo kan matsalar rashin aikin yi, ta yadda yawan masu fama da ita zai zama kasa da kashi 4.5% na jimilar al'ummar kasar. Wani sabon matakin da aka dauka a wannan shekara shi ne, sanya manoma masu ci rani a birane cikin mutanen da za a kidaya don samun ainihin adadin wadanda ke bukatar guraben aikin yi, kana ana sa ran wannan adadin ba zai wuce kashi 5.5% ba. Ta haka za a san ainihin yanayin da ake ciki a fannin samar da aikin yi a kasar Sin.
A bana, wato shekarar 2018, ake cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar bude kofa da gyare-gyare a kasar Sin, kana shekara ce ta farko da ake kokarin aiwatar da manufofin da aka tabbatar a babban taro karo na 19 na wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, saboda haka shekarar tana da muhimmancin gaske ga kokarin samar da al'umma mai walwala a kasar Sin. Cikin rahoton da aka gabatar dangane da ayyukan gwamnatin kasar Sin, an jaddada bukatar aiwatar da tunanin tattalin arzikin zaman gurguzu mai salon musamman na kasar Sin irin na sabon zamani da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tsara, da kokarin tabbatar da zaman karko, gami da neman ci gaba a lokaci guda.
Firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya kara da cewa,
"Na farko, za a yi kokarin samun ci gaba, tare da tabbatar da ingancinsa, da daidaita matsalar rashin daidaito tsakanin wurare daban-daban a fannin samun ci gaban tattalin arziki, da kokarin kyautata fasalin tattalin arzikin. Abu na biyu shi ne, kara kokarin aiwatar da gyare-gyare, da kuma kara bude kofa ga kasashe daban daban. Na uku kuma shi ne, kula da wasu fannoni 3 don samar da al'umma mai walwala, wadanda suka shafi kau da talauci, da kyautata muhallin halittu, da kuma biyan bukatun jama'ar kasar."
Haka zalika, cikin wannan rahoto, an gabatar da wasu shawarwari ga gwamnatin kasar Sin domin ta kula da su yadda ya kamata a bana, wadanda suka hada da: gyaran tsarin masana'antun kasar, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da taimakawa kokarin raya kauyuka da yankin karkara, da neman samun daidaito tsakanin tattalin arzikin wurare daban daban na kasar, da habaka cinikayya da janyo karin jarin da ake zubawa.(Bello Wang)