in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An mika shirin gyaran fuskar tsarin gwamnatin kasar Sin ga majalisar kasar domin a tantance shi
2018-03-14 13:20:36 cri

A jiya Talata, an mika shirin gyaran fuskar tsarin gwamnatin kasar Sin ga majalisar wakilan jama'ar kasar Sin domin ta tantance shi.

Kafin a kaddamar da tarukan majalissun kasar Sin dake gudana yanzu, an zartas da wasu shirye-shirye na daidaita tsarin hukumomin gwamnatin kasar a wajen taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ya gudana a karshen watan Fabarairun da ya shude. Shirye-shiryen sun shafi yin kwaskwarima ga tsarin shugabanci na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da tsarin kula da kasa na gwamnatin kasar, da tsarin aikin soja, gami da tsarin aiki na kungiyoyi daban daban na kasar. An kuma tsara shirye-shiryen ne don neman zamanintar da tsarin gwamnati na kula da kasa. Sai dai shirin da aka mika ma majalisar wakilan jama'ar kasar a wannan karo ya shafi gyare-gyare kan tsarin hukumomin kasar ne kawai.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong, ya yi bayani kan wannan shiri na gyaran fuskar tsarin gwamnati ga majalisar wakilan jama'ar kasar, inda ya ce, ana neman gyare-gyaren ne domin tabbatar da cewa gwamnati za ta dinga gudanar da ayyukanta bisa doka, da kokarin neman gamsar da jama'ar kasar. A cewar mista Wang,

"Za a sauya ayyukan gwamnati, don sanya kasuwa a maimakon gwamnati ta yadda za ta haifar da cikakken tasiri ga aikin raba albarkatu, da baiwa gwamnati damar taka rawa mai kyau a harkoki daban daban. Za a nemi ci gaban tattalin arziki mai inganci, da rufa ma gwamnatin kasar baya a kokarinta na sa ido kan kasuwanni, da kula da al'umma, da samar da hidima ga jama'a, da kiyaye muhalli, da dai makamantansu."

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, an riga an sauya fasalin majalisar gudanarwar kasar har karo 7, ta yadda hakan ya samar da wani tsarin gwamnati da ya dace da tsarin kasar na gurguzu, inda ake samun kasuwanni masu 'yanci. Sai dai bayan wadannan gyare gyare, an dade ba a sauya fasalin hukumomin gwamnatin kasar ba tun bayan shekarar 2013. Zuwa yanzu wasu matsalolin da ake fuskantar da suka hada da kafa hukumomi fiye da kima, da rashin kayyade ainihin nauyin da hukumomin za su dauka, lamarin da ya hana ruwa gudu ga kokarin kasar na neman ci gaban kasa da na al'ummarta.

Haka zalika, cikin shekarun baya, kasar Sin ta kara dora muhimmanci ga yunkuri kyautata muhallin halittun kasar. Sa'an nan don biyan bukatun kasar a wannan fanni, an yi shirin daidaita majalisar gudanarwar kasar don kafa wata sabuwar ma'aikata, wato ma'aikatar albarkatun kasa da ta halittu. Game da wannan mataki, Wang Yong ya yi bayanin cewa,

"Babban aikin wannan ma'aikata shi ne sanya ido kan yadda ake cin gajiyar albarkatun kasa da na halittu, don kokarin kiyaye su. Za a raba albarkatun zuwa gidaje daban daban, ta yadda a kowane gida za a tabbatar da cewa wane ne ke da nauyin kula da albarkatun, sa'an nan duk wanda ya yi amfani da albarkatun, dole ne ya biya kudi ga jama'ar kasar."

Ban da wannan kuma, sauran sabbin ma'aikatun da za a kafa a kasar Sin sun hada da ma'aikatar kula da muhallin halittu, wadda za ta gabatar da manufofin kiyaye muhallin halittu, da sa ido kan yunkurin dakile gurbacewar muhalli.

A fannin harkar raya tattalin arziki, za a kafa wasu hukumomi masu sanya ido kan kasuwanni, da hada-hadar kudi. A nashi bangaren, Wang Yong ya yi bayani kan nauyin wata hukumar da ake neman kafawa, wadda za ta sa ido kan aikin kasuwannin kasar, ya ce,

"Aikinta shi ne, kula da harkoki masu alaka da kasuwanni, irinsu rajistar kamfanoni, da samar da bayanan da ake bukata, da yakar ra'ayin babakere, da sa ido kan ingancin kayayyakin da ake samarwa, da dai sauransu."

Banda wannan kuma, sauran sabbin hukumomin da za a kafa a kasar Sin sun hada da kwamitin sanya ido ga aikin bankuna da harkar inshora, da hukuma mai kula da ba da tallafi ga kasashen wajen. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China