180310-gyaran-kundin-tsarin-mulkin-kasar-sin-zainab.m4a
|
Ana neman gyara aya ta 21 na kundin tsarin mulkin kasar Sin dake cikin daftarin gyaran kundin tsarin mulki da aka gabatarwa taron wakilan jama'ar kasar Sin a bana. Wakilai da dama suna ganin cewa, gyaran kundin tsarin mulkin kasar yana da ma'ana sosai. Wakilin majalisar NPC kuma magajin birnin LinCang na lardin Yunnan na kasar Zhang Zhizheng ya bayyana cewa,
"Ana son gyara kundin tsarin mulkin bisa yanayin bunkasa da bukatun kasar a halin yanzu. A matsayina na wakilin jama'ar kasar Sin ina goyon bayan aikin. Abun da ya ja hankalina sosai a cikin gyaran kundin tsarin mulkin shi ne, shigar da jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a matsayin tushen tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin, da kuma tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki. A ganina, wannan zai taimaka wajen kara hada kan kabilu daban daban da bangarori daban daban a fadin kasar. ina goyon bayan gyaran."
A cikin shawarwari 21 na gyaran kundin tsarin mulkin kasar, guda 11 sun shafi kwamitin sa ido kan gwamnatoci da hukumomin kasar. A ganin wakilan majalisar NPC, ba kwamitin sa ido kan gwamnatoci da hukumomin kasar wani iko a cikin kundin tsarin mulkin kasar shi ne babban gyaran tsarin siyasa da ikon siyasa da huldar siyasa na kasar Sin, kana ya zama muhimmin matsayi a cikin tsarin sa ido na kasar. Wakiliyar majalisar NPC kuma shugabar kamfanin lauya na Yuanduyinghe na lardin Shandong Gao Mingqin ta bayyana cewa, wannan aiki zai ba kasar Sin karfin gwiwar kara yaki da cin hanci da rashawa da raya tsarin halayyar 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar, inda Ta ce,
"Shugaba Xi Jinping yana dora muhimmanci ga aikin yaki da cin hanci da rashawa da kiyaye halayyar 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma ana samun nasarori. A mataki na gaba, ana bukatar kafa kwamitin sa ido kan gwamnatoci da hukumomin kasar yayin da ake raya kasa bisa dokoki da inganta tsarin kasar, don haka an shigar da kafa kwamitin a cikin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, da baiwa kwamitin iko a cikin tsarin mulkin kasa, wanda zai taimaka wajen tsara dokar sa ido ta kasar."
Kana Shigar da aikin sa kaimi ga kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a cikin daftarin gyaran kundin tsarin mulkin kasar ita ma ta ja hankalin jama'a sosai. A ganin wakilin majalisar NPC kuma shugaban kungiyar cinikkaya ta hanyar siliki ta kasa da kasa Lv Jianzhong, wannan gyara ya dace da moriyar jama'ar kasar Sin har ma da na jama'ar duniya gaba daya, kuma duniya za ta amince da wannan aiki. Mr Lv ya bayyana cewa,
"Shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', wadda ta dace da moriyar jama'ar kasashen duniya, don haka an samu nasarori wadanda suka zarce zaton da aka tsara. Domin tunanin 'ziri daya da hanya daya' shi ne hadin gwiwa cikin lumana da bude kofa ga kasashen waje da koyi da juna da musayar fasahohi da samun moriyar juna, ta haka za a kafa wani dandali ne daukar nauyi iri daya, da moriya iri daya da kuma buri iri daya, wanda ya dace da yanayin da ake ciki a yanzu, da moriyar jama'ar kasar Sin da ta kasashen duniya gaba daya, kuma kasa da kasa za su amince da shi."
Bisa ajandar taron, wakilan majalisar NPC kimanin dubu 3 za su jefa kuri'a game da daftarin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, za a zartas da shi idan kashi 2 cikin 3 na wakilan majalisar NPC suka goya masa baya. (Zainab)