in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: dole ne a aiwatar da manyan tsare-tsaren bunkasa yankunan karkara
2018-03-09 10:43:57 cri

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar Mr. Xi Jinping, ya ce aiwatar da manyan tsare-tsaren raya yankunan karkara, muhimmin aiki ne da JKS ta kaddamar a yayin babban taron wakilanta karo na 19, sannan babban aiki ne da ke kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni da kafa kasa ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni.

Shugaba Xi Jinping wanda ya bayyana haka yayin da ya halarci taron tattauna rahoton aikin gwamnati da aka gabatar, wanda kungiyar wakilan jama'ar lardin Shandong ta shirya a jiya, ya kara da cewa, raya yankunan karkara gaggarumin aiki ne da zai bunkasa aikin gona da manoma yadda ya kamata, a wannan sabon zamani.

"Yau ce ranar 8 ga watan Maris, wato ranar mata ta duniya. A madadin kwamitin tsakiya ta jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ina son in tayawa mata wakilan jama'a da 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasa da ma'aikata da dukkan matan kasar nan a sassa daban daban da kuma kabilu daban daban murna tare da yi muku fatan alheri."

A jiya da safe, Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa kan rahoton aikin gwamnati da aka gabatar wadda kungiyar wakilan jama'ar lardin Shandong ta shirya. A daidai wannan lokaci, Xi ya nuna fatansa ga mata 47 wakilan jama'a da ke kungiyar Shandong da ma dukkan matan kasar.

A yayin da mista Gong Zheng ya ambato ra'ayin samun sa'a da rabo a lokacin da ake kyautata raya kasa, Xi Jinping ya jaddada cewa, "Idan mun ambato samun sa'a da rabo yayin da muke gudanar da wani babban aiki, ba ma nufin nuna kasala kan aikinmu, ko kuma rashin bukatar kokari, a'a, dole ne mu bi madaidaicin ra'ayi kan sa'a da rabo. Dole ne mu kawo wa fararen hula alheri na a-zo-a-gani, kana mu yi hangen nesa, mu dasa harsashi mai kyau, mu kuma share fage wajen ci gaba da gudanar da aiki yadda ya kamata. Ma iya cewa, muna kokarin samun ci gaba na a-zo-a-gani, yayin da muke share fage domin kara samun ci gaba a nan gaba. Kada mu mayar da samun sa'a da rabo gaba da komai. Za mu nemi samun amincewa daga fararen hula, da kuma ainihin ra'ayin jama'a a tarihi."

Zhang Shuqin, wata malama ce da ke aiki a yankin Yimeng, inda aka taka muhimmiyar rawa a yakin mahara sojojin Japan da kuma yakin neman 'yantar da jama'ar kasar ta Sin. Ta yi magana kan yadda za a ilmantar da kananan yara al'adun gargajiya. Xi Jinping ya saurari maganarta, ya kuma bayyana cewa, "Tilas ne a gaji al'adun gargajiyarmu daga zuriya zuwa zuriya. A makarantunmu, musamman ma a makarantun firamare da ta midil, wajibi ne mu mai da hankali kan ilmantar da yara manyan gobe al'adun gargajiya. Kada su zama masu rashin godiya ga magabatanmu da kasarmu. Tilas ne mu karfafa karfinmu a wannan fanni. Wajibi ne yaranmu su tuna da yadda al'ummar Sin suka yi gwagwarmaya domin tsayawa da kafafunsu, sun yi kokarin samun wadata, suna kuma karfafa karfinsu da kwarewarsu. Al'ummar Sin suna ta fito da abubuwan na ban mamaki."

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya amince da ayyukan da lardin Shandong ya yi bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, ya kuma yi fatan cewa, mutanen lardin na Shandong za su ci gaba da kokarinsu, su zama kan gaba wajen raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni da kuma raya kasar Sin ta zamani mai tsarin gurguzu a sabon zamani.

Lardin Shandong, babban lardi ne wanda ya dade da shahara a fannin aikin gona. Xi Jinping ya bukaci Shandong da ya aiwatar da manyan tsare-tsaren bunkasa yankunan karkara yadda ya kamata. "Aiwatar da manyan tsare-tsaren raya yankunan karkara, muhimmin aiki ne da JKS ta kaddamar a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, kuma babban aiki ne da ke kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni, da kafa kasa ta zamani mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, kana gaggarumin aiki ne wajen bunkasa yankunan karkara, aikin gona da manoma yadda ya kamata a sabon zamani. Da tabbatar da ganin an kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni da kuma kafa kasa ta zamani da gurguzu, ta dogaro da ci gaban aikin gona, bunkasuwar yankunan karkara da kudaden shiga da mamona suke samu. Don haka wajibi ne mu fahimci muhimmanci da wajibcin aiwatar da manyan tsare-tsaren raya yankunan karkara, sannan mu dauki hakikanin matakai wajen aiwatar da manyan tsare-tsaren." (Tasallah Yuan)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China