in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi bayani kan manufar kasar a fannin diplomasiyya
2018-03-08 19:54:42 cri

A yau Alhamis ne aka kira wani taron manema labaru a yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi bayani kan burin da kasar ta sanya a gaba a kokarinta na inganta hulda da kasashen waje, da makomar shawarar "ziri daya da hanya daya", da yanayin da kasar Sin ke ciki a fannin harkar diplomasiyya, da dai sauransu.

Tun a wannan shekarar 2018 ce aka fara kokarin aiwatar da manufofin da aka tsara a bara yayin taron wakilan 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, don haka Wang Yi ya fara bayani kan manufar da aka gabatar yayin, wato burin kasar Sin na inganta hulda da sauran kasashe a matsayin ta na babbar kasa, tare da nuna wani salon musamman na kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, inda ya ce,

"A watan Oktoban bara, babban magatakardan kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada a cikin rahoton da aka gabatar yayin taron wakilan 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cewa, kasar Sin za ta yi kokari tare da sauran kasashe a sabon nau'in huldar kasa da kasa, da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummar duniya , wannan shi ne burin kasar Sin a fannin diplomasiyya a sabon zamanin da muke ciki. Bisa wannan burin da aka sanya gaba, kasar Sin za ta yi kokarin kyautata yanayin da take ciki a fannin hulda da kasashen waje. Kana za ta yi kokarin samar da gudunmowa ga yunkurin kyautata rayuwar dan Adam a duniya."

Ban da haka, yayin da kasar Sin take kara habaka tasirinta a fadin duniya, sai wasu suke zargin cewa, kasar tana kawo barazana ga sauran kasashen duniya. Dangane da wannan batu, mista Wang Yi ya ce wannan magana karya ce kawai.

A cewarsa,

"Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen karuwar tattalin arzikin duniya da kuma yaki da talauci, kana tana ba da karin gudummowa wajen kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, ban da haka kuma, kasar Sin ta bullo da shawarar ziri daya da hanya daya, domin gudanar da harkokin duniya tare da sauran kasashe yadda ya kamata. Dangane da gudunmawar da kasar Sin ta bayar a duniya, abin da za a iya gani daga ciki shi ne damammaki a maimakon barazana."

Har ila yau, mista Wang Yi ya yi bayani kan makomar shawarar da kasar Sin ta gabatar ta "ziri daya da hanya daya", inda ya ce, yanzu haka akwai kasashe da yankuna fiye da 80 da suka sa hannu kan yarjejeniyar aiwatar da hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Bisa wannan shawara, ana kokarin samar da kayayyakin more rayuwa da yawa a kasashe daban daban, inda ake daukar kayayyakin a matsayin damar raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma. Wang Yi ya kara da cewa,

"Hadin kai game da shawarar "Ziri daya da hanya daya", ko a fannin bullo da shirye-shirye, ko yadda ake gudanar da hakikanan ayyuka, dukkansu an yi su ne a bayyane. Babu bangaren da ya fi wani, a maimakon haka bangarori daban daban sun shiga ayyukan bisa zaman daidai wa daida, kuma ba a gudanar da ayyuka a boye ba, a maimakon haka ana gudanar da komai ne a fili, kana kowane bangare yana samun moriya, don haka shawarar wata dama ce ta samun moriya da nasarori tare."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China