180306-Xi-Jinping-na-fatan-yankin-Mongolia-na-gida-zai-yi-kokarin-raya-tattalin-arziki-mai-inganci-tare-da-kawar-da-talauci-daga-yankin.m4a
|
"Har yanzu muna cikin watan farko na kalandar gargajiya, wato har yanzu ana murnar sabuwar shekara. Ina fatan dukkan wakilai da jami'ai da al'ummomin yankin Mongolia na gida suna cikin farin ciki da koshin lafiya, kuma ina yi wa 'yan Mongolia na gida miliyan 25 fatan alheri a wannan shekarar ta kare."
A watan Janairun bana ne, a yankin Mongolia na gida aka zabi Mr. Xi Jinping a matsayin wakilin babban taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13. A lokacin da ya tabo dalilin da ya sa aka zabe shi a yankin Mongolia na gida, shugaba Xi Jinping ya ce, "Dalilin da ya sa na zama wakilin jama'a a yankin Mongolia na gida shi ne, ina fatan wannan zai bayyana yadda kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yake mai da hankali kan yankuna masu kabilu da dama wadanda suke kan iyakar kasa da kasa, da niyyar kwamitin kolin jam'iyyar ta bunkasa yankuna marasa arziki, tare da yin namijin kokari wajen samun nasarar kawar da talauci daga yankunan."
Bayan ya saurari ra'ayoyin da sauran wakilai 8 suka gabatar kan yadda za a bunkasa yankunan karkara, da sha'anin yawon bude ido da kawar da talauci da dai makamatansu, Xi Jinping ya nuna cewa, an riga sauran yankuna kafa yankin Mongolia na gida mai cin gashin kansa, kuma an riga sauran yankuna aiwatar da dokokin mulkin kansu a yankunan kananan kabilu a nan kasar Sin. Yankin Mongolia na gida yana da muhimmanci sosai sabo da yana kan iyakar kasa da kasa a arewacin kasar. Shugaba Xi Jinping ya tabbatar da sabuwar nasarar da yankin Mongolia na gida ya samu cikin shekaru 5 da suka gabata. Game da batun kawar da talauci daga yankin Mongolia na gida, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a lokacin da ake kokarin shawo kan matsalolin da ake fuskanta yanzu, dole ne a mai da hankali wajen kafa babban shirin neman ci gaba mai dorewa a nan gaba. Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Ya kamata a hada aikin yaki da talauci da shirin bunkasa yankunan karkara, ta yadda za a iya tabbatar da ganin yankunan karkara masu aikin noma da kiwo sun samu ci gaba a cikin yanayi na zamani, amma maras gurbata muhalli. Makiyaya da manoma za su iya samun arziki. Bugu da kari, dole ne a sa ido kan matsalolin cin hanci da rashawa a lokacin da ake fama da talauci. Dole ne kuma a hukunta wadanda suke yunkurin cin kudin shirin yaki da talauci."
Kawo yanzu, ana da kabilu 55, wato mutane fiye da miliyan 25 a yankin Mongolia na gida mai cin gashin kansa, daga cikinsu, 'yan kananan kabilu sun kai kashi 1 bisa biyar. Shugaba Xi Jinping yana fatan kabilu daban daban da suke zaune a yanki daya za su kara hada kai domin tsaron kan iyakar kasa da kasa, da kuma jin dadin kyakkyawar zaman rayuwa tare.
Yankin Mongolia na gida yana da wakilai 57 da suke halartar babban taron wakilan jama'ar kasar Sin. Bayan sun dudduba rahoton aikin gwamnati tare da Mr. Xi Jinping, Mr. Feng Yuzheng, wani wakilin jama'a na yankin Mongolia na gida ya bayyana cewa, "Babban sakatare Xi Jinping ya dudduba rahoton aikin gwamnati tare da sauran wakilai na yankin Mongolia na gida a yau, wannan ya bayyana yadda babban sakatare Xi yake begen al'ummomi miliyan 25 na kabilu daban daban na yankinmu, da kuma yadda babban sakatare Xi yake mai da hankali kan yadda yankunan dake kan iyakar kasa da kasa suke samun ci gaba. Tabbas, za mu yi kokarin sauke nauyin da aka dora mana domin jin dadin jama'ar da muke wakilta." (Sanusi Chen)