180321-taruka2-tasallah.m4a
|
A yayin taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a jiya, mista Han Wenxiu ya yi bayanin cewa, baya ga karin shawarwari da aka bayar dangane da takaitaccen bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 5 da suka wuce, da kuma ayyukan gwamnatin kasar, rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin ya bayar da karin shawarwari kan ayyukan da za a gudanar a bana. Han Wenxiu ya ce, "An tanadi 'gaggauta raya sana'ar ba da hidima ta zamani' da 'kafa zaman al'umma mai hikima' cikin bangaren bunkasa sabon karfin raya tattalin arziki. An kuma tanadi 'kara azama kan aikin kera kayayyaki bisa ilmi da basira', da 'yayyata kyawawan halayen 'yan kwadago a matsayin abun misali', da kuma 'horas da 'yan kwadago masu ilmi, fasaha da ra'ayin kirkire-kirkire' cikin bangaren gaggauta raya kasa mai karfin kera kayayyaki. Sa'an nan kuma, an tanadi 'sa kaimi kan kafa wuraren gwaje-gwaje da yin gyare-gyare kan tsarin yin alkawari dangane da zuba jari' da 'inganta kafa ma'aunin ba da hidimar gwamnati' cikin bangaren zurfafa gyare-gyaren da ake yi kan yadda gwamnatoci a matakai daban daban za su kyautata ba da hidima ta wasu hanyoyi."
Har wa yau, dangane da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, rahoton ayyukan gwamnatin ya yi tanadin "yin gyare-gyare kan tsarin sa ido kan harkokin kudi" da "daga matsayin bunkasuwar shiyyoyin hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki a bakin iyakar kasa da kuma ketaren iyakar kasa".
Mista Han ya yi karin bayani da cewa, an kuma mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a cikin rahoton ayyukan gwamnatin. "An tanadi 'dora muhimmanci kan kulawa da horas da malamai masu koyar da kananan yara', da 'kara karfin horas da likitoci da ma'aikatan jinya', 'da sanya rigakafin barkewar munanan cututtuka a gaba da komai tare da inganta sa ido kansu', da 'kulawa da kuma taimakwa kananan yara da ke zaune a yankunan karkara, wadanda iyayensu ke ci rani a sauran wurare', da 'inganta ba da tabbaci ga kananan yara da ke cikin mawuyancin hali', da 'gaggauta raya masana'antun al'adu', da 'karfafa gwiwar jama'a wajen karatu ' da dai sauransu. "
Ban da haka kuma, Han Wenxiu ya yi nuni da cewa, a bana kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan neman ci gaba ba tare da tangarda ba. Yayin da take bunkasa tattalin arzikinta ba tare da wata matsala ba, a kokarin tabbatar da bunkasar tattalin arziki yadda ya kamata, za ta kuma yi gwagwarmaya wajen raya tattalin arziki da kyau."Za mu ci gaba da kyautata tsarin tattalin arziki a bana. Za kuma mu fito da karin sabbin matakai a fannin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare. Musamman ma yayin da za a cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin a bana, za a gudanar da wasu bukukuwa domin murna. A ganina, hanya mafi dacewa da za mu bi wajen tunawa da cika shekaru 40 da aiwatar da wannan manufa ita ce, rubanya kokarinmu na daukar matakan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Har ila yau, za mu ci gaba da kyautata zaman rayuwar jama'a, tare da kyautata muhalli da yanayi. "(Tasallah Yuan)