180312-An-zartas-da-gyaran-kundin-tsarin-mulkin-kasar-Sin-Bilkisu.m4a
|
A yayin zaman taro na uku na taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, 'yan majalisar 2964 sun jefa kuri'a ba tare da sanya suna ba, kan gyaran kundin tsarin mulki, inda aka samu kuri'un amincewa 2958, na adawa 2 da kuma na janye jiki 3. Bisa abubuwan da aka tanada game da jefa kuri'a kan kudurori a yayin taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar karo na 13, za a zartas da gyaran kundin tsarin mulkin ne ta hanyar jefa kuri'u ba tare da sanya suna ba, kuma za a iya zartas da shirin idan an samu kuri'u sama da kashi 2 cikin 3 na dukkan 'yan majalisar. Don haka, a wannan rana, majalisar koli ta taron, ta sanar da gyaran kundin tsarin mulki da kuma gudanar da shi.
A yayin taron manema labaru da aka shirya bayan taron, daraktan kwamitin kula da ayyukan dokokin shari'a na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Shen Chunyao ya bayyana cewa, an gyara kundin tsarin mulkin ne bisa kiyaye dokoki, wanda ya cimma burin shigar da wasu manyan manufofi da ra'ayoyi da aka tabbatar a yayin taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cikin wannan babbar dokar kasa. Ko shakka babu zartas da gyaran kundin tsarin mulkin zai inganta tare da ba da tabbaci wajen samun ci gaban harkokin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na kasar.
Sabon gyarararren kundin tsarin mulkin na kunshe da ayoyi 21, inda aka tabbatar da matsayin shugabancin na tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulkin na gurguzu mai hayalayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki wajen gudanar da harkokin siyasa da zaman takewar al'umma. Game da haka, Shen Chunyao ya ce,
"Tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani, sabuwar nasara ce da aka samu wajen kyautata hasashen Marxism don dacewa da halin kasar Sin, ita ce kuma babbar manufar dake jagorantar nasarar da aka cimma da manyan sauye-sauye da aka yi kan harkokin jam'iyyar kwaminis da na fadin kasar tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18. Nuna sabbin nasarori da jama'ar kasar suka samu a karkashin jagorancin shugabannin kasa, wani abu ne na musamman ga kundin tsarin mulkin kasar Sin, wato muhimmiyar fasaha ce da muka samu wajen raya tsarin mulkin kasa."
Game da cire wata aya dake kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar, wato wadda ta ce ba a iya dale kujerar shugabancin kasar da mataimakin shugaban kasa fiye da sau biyu, Shen Chunyao yana ganin cewa, wannan na da amfani ga kyautata tsarin shugabancin kasar Sin, da kuma gudanar da harkokin jam'iyyar da na kasar yadda ya kamata. Ya ce,
"Mutum daya kacal na rike kujerun koli guda uku, wato shugaban kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da shugaban kwamitin soja na tsakiya da kuma shugaban kasa, irin wannan tsarin shugabancin ya zama abu na dole, kuma mafi dacewa ga babbar jam'iyyarmu da babbar kasarmu. Gyara wannan aya dake cikn kundin tsarin mulki wani muhimmin mataki ne na kyautata tsarin shugabancin kasar, zai yi amfani wajen karfafa martabar da gwamnatin tsakiya take da ita karkashin jagorancin Xi Jinping, da kuma tabbatar da zaman karkon jam'iyyar da zaman takewar kasar mai dorewa. "
Abun da ya kamata a lura da shi shi ne, gyararren kundin tsarin mulki na kunshe da ayoyi 21, kuma 11 daga ciki sun shafi kwamitin sa ido. Game da haka, mataimakiyar daraktan kwamitin kula da ayyukan dokokin shari'a na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zheng Shuna ta ce,
"An zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin sa ido ne da nufin kara karfin yaki da cin hanci da rashawa, da karfafa jagorancin jam'iyyar a fannin, da kuma kafa ingantaccen tsarin sa ido. Wani muhimmin aiki daga ciki shi ne, kafa kwamitin sa ido, wanda hakan, zai inganta ayyukan tsaftace jam'iyyar da zurfafa ayyukan yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda za a kara samun ci gaba. " (Bilkisu)