Rukunin masanan kimanta kan batun Ebola ya gabatar da wani rahoton farko bisa rogon hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO a Geneva, inda ya ba da shawara ga hukumar da ta daga karfinta na ba da jagoranci, da taimakawa mambobinta ta fuskar inganta tsare-tsaren kiwon lafiyarsu, don inganta kokarin tinkarar cutar da ta zo ba zato ba tsammani, ciki hadda Ebola.
Rahoton kuma ya nuna cewa, WHO ba ta da isashen karfin tinkarar halin ko ta kwana ta fuskar kiwon lafiya, a cewar wannan rahoto, ya kamata a kara karfin ba da jagoranci na WHO a cikin harkokin kiwon lafiya na kasa da kasa, da kuma kafa wata hukuma ta kanta don tinkarar halin ko ta kwana da wani asusu domin daidaita masifar da za a gamu ba zato ba tsamani, sannan a kara hadin gwiwa da sauran hukumomin MDD, da horar da rukunonin dake mallakar fasahohi daban-daban, kana a taimakawa mambobinta wajen inganta tsare-tsarensu na kiwon lafiya. (Amina)