in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an MDD sun bukaci karin kudi domin magance Ebola baki daya
2015-02-06 09:46:21 cri

Manyan jami'an MDD da na hukumar lafiya ta duniya WHOn a ranar Alhamis din nan suka bukaci karin kudade domin taimakawa magance barkewar cutar Ebola, ganin yadda aka samu sabon bular shi a makon jiya a yankin yammacin Afrika.

Babban manzon majalissar a kan cutar Ebola David Nabarro ya shaida wa manema labarai cewar, kasashen duniya sun yi iyakacin kyautatatawa daga mutane masu zaman kansu, gwamnatoci, kungiyoyi masu zaman kansu da 'yan kasuwa wajen ba da gudunmuwarsu.

Daga watannin Oktoba zuwa Disambar bara, an kashe fiye da kudi dalar Amurka miliyan 850 a yaki da cutar, a cewar Mr. Nabarro, kuma sakamakon haka, an samu ci gaba sosai, sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba a kan barazanar da cutar ke haifarwa.

Ya yi gargadin cewar, an fara samun karuwan wadanda ke dauke da cutar a makon da ya gabata, an tabbatar da wassu 124 sabbin kamu, abin da ya nuna karuwar cutar da kashi 25 a cikin 100 idan aka kwatanta da makonnin baya.

Manzon na musamman a kan cutar Ebola ya yi bayanin cewa, za'a ci gaba da aiki tukuru har sai an ga cewar mutum na karshe mai dauke da cutar ya samu warka kuma cutar ta daina yaduwa.

A cewar David Nabarro, daga watannin Janairun zuwa Yunin wannan shekarar, ana bukatar kudi dalar Amurka biliyan 1.5 domin yakar cutar domin a yanzu ana da tazarar dalar biliyan 1. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China