Wasu sabbin rahotanni biyu da babban bankin duniya ya fitar sun bayyana irin mummunan tasiri da cutar Ebola ke haifarwa ga kasashen Liberiya da Saliyo a yanzu da ma nan gaba.
Hakan, a cewar kakakin MDD Farhan Haq abu ne a fili, idan aka kalli yadda cutar ta haifar da raguwar ayyukan yi da dama a kasar Liberiya. Haq wanda ke tsokaci game da rahoton dake kunshe da bayanai game da yadda wannnan matsala ta fi shafar mata, da ma yadda hakan ke barazana ga harkokin noma, ya ce, annobar cutar Ebola ta jefa kasashen biyu cikin wani mawuyacin yanayi.
Ya ce, a Saliyo, rahotannin sun nuna cewa, masu aikin albashi, da sauran masu sana'u daban daban da ba su shafi noma ba, su ne rukunin da suka fi fuskantar raguwar ayyukan yi a birane.
Bisa kiyasi, rahoton ya nuna cewa, masu aikin albashi 9,000, da kuma masu sana'un hannu 170,000 ne suka rasa ayyukan yi daga watan Yuli zuwa watan Agustan shekarar da ta gabata.
Kaza lika akwai alamu na rashin tabbas game da samun abinci, da kuma raguwar masu zuwa asibitoci saboda wasu cututtukan da ba su shafi Ebola ba a birnin Freetown, fadar gwamnatin kasar ta Saliyo.
A wani batun mai alaka da wannan kuma, shirin samar da abinci na duniya WFP, ya yi kashedin cewa, adadin mutanen dake fuskantar karancin abinci sakamakon cutar Ebola, na iya kaiwa miliyan daya nan da watan Maris mai zuwa, muddin ba a kara samar da hanyoyin wadata al'ummun kasashe 3 da wannan cuta ta fi shafa, su sama da 720,000 da abincin ba. (Saminu)