Ministan wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce, za a fara aiwatar da shirin duba lafiyar fasinjojin ne a mako mai zuwa yayin da aka himmatu wajen samar da dukkan abubuwan da ake bukata, kamar ma'aikata da kayayyakin aiki.
Chukwu ya kuma shaidawa 'yan jaridun cewa, darasin da Najeriya ta koya ya kara bude wa kasashen duniya ido game da tabbacin cutar ta Ebola, wadda ya zuwa wannan lokaci ta halaka mutane biyu a Najeriya.
Najeriya ta yanke shawarar fara duba lafiyar fasinjoji kafin su bar kasar ne kasa da sa'o'i 24 bayan da kasar ta Najeriya ta ayyana dokar ta baci game da cutar Ebola, ganin yadda yanzu kowa a duniya ke cikin barazana.
A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, mutane 1,711 ne suka kamu da cutar, kana 932 suka mutu a wannan shekara a cikin kasashen Guinea, Liberia, Najeriya da Saliyo. (Ibrahim)