in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola ta bulla a tsakiyar Scotland
2014-12-30 10:56:35 cri

A yanzu haka a kasar Scotland, an tabbatar da cewar, wata ma'aikaciyar kiwon lafiya da ta isa babban birnin Scotland Glasgow a ranar Litinin daga kasar Saliyo ta kamu da cutar Ebola.

Wata sanarwar gwamnatin Scotland ta bayyana cewar, ma'aikaciyar kiwon lafiyar wacce ta iso Scotland a cikin jirgin saman Britaniya, wanda ya yi zango a Casablanca ta kasar Morocco da kuma birnin London, a karshe ya isa Scotland a ranar Lahadi, to amma ita ma'aikaciyar kiwon lafiyar, an kwantar da ita a ranar Litinin a asibitin Gartnavel dake Grasgow a karkashin bangaren cututtuka masu yaduwa a sakamakon korafin da ta yi a kan bata jin dadin jikinta.

Sanarwar ta ce, a yanzu an killace maras lafiyar bayan an gano tana dauke da kwayar cutar Ebola, saboda kulawa da kuma kare cutar daga yaduwa.

A yanzu asibitin na binciken dukanin wadanda suka yi hulda da maras lafiyar, kuma duk wanda aka gano cewar, yana cikin barazanar kamuwa da cutar, to asibitin kwararru zai tuntube shi domin daukar matakan lafiyar da suka dace.

Sanarwa ta ce, babu wata barazana ga sauran jama'a, musamman saboda an samu sa'a na gano cutar a jikin ma'aikaciyar tun kafin cutar ta yi nisa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China