Ranar 25 ga wata kasancewarta ta kasance ranar yaki da zazzabin cizon sauro a duniya bisa taken "Yin rigakafi da kawar da zazzabin cizon sauro". WHO ta nuna cewa, tun a shekarar 2000, bisa kokarin da aka yi a duniya na kawar da wannan cuta ya taimaka wajen kare mutane kusan miliyan 3.3 daga mutuwa sanadiyyar wannan cuta, kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon wannan cuta ya ragu a duniya da kashi 42 cikin dari sannan a Afrika da kashi 49 cikin dari. (Amina)