Babbar darektar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Margaret Chan a ranar Alhamis din nan ta yaba saurin farfadowar da kasashen da annobar Ebola ta shafa na yammacin Afrika wadda ta ce, sun yi iyakacin kokarinsu, abin da ya sa take neman wassu hanyoyi da za su kara taimaka musu farfadowa gaba daya.
Madam Chan ta sheda wa manema labarai a Washington na Amurka cewa, makasudin ayyukan saurin farfadowar shi ne a taimaka wa jama'a da al'ummarsu komawa rayuwa na yau da kullum, wanda ke nufin yara za su koma makaranta, mata za su koma sayayya a kasuwannin unguwanninsu da sauran rayuwa da aka saba.
Ta ce, babban muhimmin dawo da rayuwan yau da kullum shi ne sake gina manyan ayyukan samar da kiwon lafiya da hidimomi a wadannan kasashen wadanda a baya suka ruguje, dalilin annobar da kuma shekaru da daman a fuskantar tashin hankali.
A ta bakinta, dole ne a mai da hankali wajen karfafa sha'anin kiwon lafiya.
Shugabar ta WHO ta kuma bayyana ayyukan kiwon lafiya a matsayin kula da cibiyoyin shan magani na unguwanni da kuma samar da wani shiri na sa ido wanda zai ba da rahoton duk wata sabuwar matsala da ka iya kunno kai domin isar da gargadi cikin lokaci. (Fatimah)