Ismael ya kara da cewar daga cikin kasashen ukku inda cutar ta fi kamari, kasar Liberia ta fi sauran kasashen biyu samun ragowar adadin yawan jama'ar dake harbuwa da cutar ta ebola, alal misali kididdiga na nuni da cewar a Liberia an samu ragowa daga yawan jama'a 300 a duk mako a watan Agustar bara ya zuwa mutane kasa da 10 kacal a duk sati a watan satumba
Hakazalika adadin yawan masu kamuwa da cutar Ebola a Saliyo da Guinea ya ragu matuka tun daga watan yuli da Agusta na shekarar bara. To amma Ismael ya ce a yayin da ake samun raguwar mutanen dake kamuwa da cutar sai kuma cutar ta yadu zuwa wasu wurare nesa da inda cutar ta bulla tun asali, hakan ya sa magatakardan MDD Ban Ki-moon daukar mataki na baiwa kasashe shawarwari da su kaucewa sakaci wajen yaki da cutar Ebola. (Suwaiba)