Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da shirin samar da abinci na MDD (WFP) sun shiga sahun yakin da ake na kakkabe cutar Ebola a yammacin Afirka.
Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ya ce, matakin ya kunshi hadin gwiwar kwararrun hukumomin biyu ne a bangaren kiwon lafiya da kayayyaki da ake yi a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo da cutar ta fi kamari.
Ya ce, jami'an hukumomin biyu za su yi amfani da na'urori ne kamar wayoyin salula, kwanfuta da Internet don musayar muhimman bayanai a kokarin da ake na hana yaduwar kwayoyin cutar a gundumomin da har yanzu ake fama da cutar.
Hadin gwiwar hukumomin tamkar amsa umarnin da shugabannin hukumar zartaswar MDD na musamman kan yaki da cutar Ebola ne suka bayar kan bullo da sabbin hanyoyin karfafa ayyukan kiwon lafiyar jama'a.
Kimanin mutane 24,000 ne cutar ta shafa tun lokacin da ta barke a kasashen yammacin Afirka, inda kusan mutane 10,000 suka mutu, galibin su a kasashen Guinea, Liberia da kuma Saliyo. (Ibrahim)