Wani nau'in maganin gargajiya na kasar Sin mai suna Tetrandrine, ka iya zamowa sahihin maganin cutar Ebola, bayan da wani binciki da aka gudanar a Amurka ya nuna tasirin maganin a jikin beraye.
Wasu masu binciken magunguna na kasar Amurka da Jamus ne suka bayyana hakan, suna masu cewa, maganin na dakile bazuwar kwayoyin cutar Ebola cikin kwayoyin halittar jikin wanda ya harbu da ita.
Bisa wannan sakamako ne jagoran tawagar masu binciken Robert Davey, ya ce, suna da kyakkyawan fatan samun karin nasara a aikin da suke gudanarwa, musamman a wannan gaba da ake ta kokarin samar da magunguna, da rigakafin cutar ta Ebola a sassan duniya daban daban. (Saminu)